Kai tsaye: Yadda Wasar fidda gwanin Qatar 2022 tsakanin Najeriya da Liberia ke gudana
- Yan kwallon Najeriya Super Eagles na karawa da yan kwallon kasar Liberiya yanzu haka a babban filin kwallon dake Surulere Legas.
- An fara wasan misalin karfe 5 na rana
- Bayan wannan wasan da kwana hudu, Najeriya zata sake bugawa da kasar Cape Verde
An tashi wasa 2-0
Bayan mintuna casa'in ana fafatawa, Najeriya ta samu nasarar lallasa kasar Liberiya a wasan fidda gwanin gasar kwallon kofin duniya da za'a buga a kasar Qatar 2022
An sako Ahmed Musa da Shehu Abdullahi
Kyaftin na Super Eagles, Ahmed Musa ya maye gurbin Leelechi Iheanachi wanda yaci kwallaye biyu., yayinda Abdullahi Shehu ya maye gurbin Alex Iwobi
Najeriya tayi sauyin dan wasa
Victor Osimhen ya fita, Paul Onuachu ya shigo
'54 Sauran Kiris Alex Iwobi yaci ta uku Kwallo
Mai tsaron ragar Liberia yayi akwati, sauran kiris dan kwallon Najeriya, Alex Iwobi, ya zura ta
An dawo hutun rabin lokaci
Bayan hutun minti 15, an dawo hutun rabin lokaci. Daga dawowa sauran kiris Victor Osimhen ya kara zuwa kwallo daya amma kwallon ya tashi sama.
Najeriya ta zira kwalle biyu yayinda aka tafi hutun rabin lokaci
Dan wasan Najeriya kuma mai takawa kungiyar Leicester leda, Kelechi Iheanacho ya zira kwalle biyu ragar Liberia.
Iheanacho ya ci kwallon farko a minti 22 da fara wasa yayinda yaci kwallo ta biyu ana gab da tafiya hutun rabin lokaci.