An saki sunaye da hotunan Sojin Amurkan da harin Bam ya kashe a Afghanistan ranar Alhamis
- Gwamnatin Amurka ta bayyana adadin jami'an da ta rasa sakamakon harin Bam a Afghanistan
- Amurka na cigaba da kwasan yan kasarta da kuma wasu yan Afghanistan da suka taimaka mata
- Sunaye da hotuna wasu daga cikin Sojoji da aka kashe sun fito
Amurka - Sunaye da hotunan jami'an Sojin Amurka 13 da suka rasa rayukansu a harin kunar bakin wake da yan ta'addan ISKP suka kai wajen tashar jirgin Kabul ranar Alhamis sun fara fitowa.
An tura wadannan Sojoji ne don duba yadda ake kwasan yan Amurka daga Afghanistan.
Sunan wani jami'in Sojin ruwa da Marine hudu sun fito yayinda har yanzu ba'a bayyana sunayen sauran Marine 6 da Sojin kasa biyu ba saboda ba'a sanar da iyalansu ba tukun.
Mai magana da yawun rundunar Marine na Amurka, Manji Jim Stenger ya bayyanawa ThePost cewa:
"Muna cigaba da jimamin mutuwar wadannan jami'ai kuma muna addu'a ga iyalansu. Abinda muka mayar da hankali kai yanzu shine kula da iyalansu da kuma wadanda suka jikkata."
Bisa tsarin Amurka, hukumar Soji ba ta sakin sunayen matattunsu sai bayan awanni 24 da sanar da iyalansu, amma wasu yan uwansu sun tabbatar da sunayen wasu daga cikinsu.
Ga jerin sunayen da suka bayyana kawo yanzu:
1. Maxton Soviak
2. Kareem Nikoui
3. David Lee Espinoza
4. Rylee McCollum
5. Jared Schmitz
Sojojin Amurka 13 suka rasa rayukansu a harin Bam da aka kai Afghanistan
Akalla dakarun Sojin Amurka 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin kunar bakin wake da ake zargin yan ta'addan ISIS suka kai tashar jirgin saman Afghanistan.
Shugaban rundunar Sojin Amurka dake kasashen waje, Kenneth "Frank" McKenzie, ya bayyana hakan a hira da manema labarai, CNN ta ruwaito.
McKenzie yace yan kunar bakin wake biyu ne suka fara kai hari sannan kuma wasu yan bindiga suka bude wuta.
Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya lashi takobin binciko wadanda suka aikata wannan ta'adi inda yan Amurka 13 suka mutu kuma 18 suka jikkata.
Asali: Legit.ng