Yanzu-yanzu: Shahrarren dan wasa, Cristiano Ronaldo ya koma Manchester United

Yanzu-yanzu: Shahrarren dan wasa, Cristiano Ronaldo ya koma Manchester United

  • Bayan shekaru 12 da barin Manchester, babban dan kwallo Ronaldo ya koma gida
  • Wannan ya faru ne yayinda ake maganar cewa zai koma ManCity a taka leda
  • Yanzu haka an fara duba lafiyarsa don tabbatar da kalau yake lafin a kammala kwantiragin

Kungiyar kwallon Manchester United dage kasar Ingila ta sanar da cewa tsohon dan wasanta, Cristiano Ronaldo, ya dawo gida bayan shekara da shekaru.

Manchester ta yi wannan sanarwa ne da yammacin Juma’a, 27 ga watan Agusta, 2021 a shafinta na Facebook.

Ronaldo da kansa ya sanar da cewa ya ajiye tala leda a kungiyar kwallon Juventus a yau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng