Nan da watanni uku, Taliban zata kwace babbar birnin Afghanistan gaba daya: Amurka

Nan da watanni uku, Taliban zata kwace babbar birnin Afghanistan gaba daya: Amurka

  • Taliban na gab da korar gwamnatin Afghanistan daga birnin tarayyar Kabul
  • Kawo yanzu Taliban ta kwace garuruwa guda tara
  • Wannan na faruwa tun bayan fitar Sojoji Amurka daga kasar

Yan kungiyar Taliban zasu iya kwace babbar birnin Afghanistan, Kabul, nan da kwanaki 90 sabanin yadda akayi tunani a baya, Reuters da Washington Post suka ruwaito, bisa wani rahoton leken asiri na Amurka.

Kungiyar ta kwace jihohi tara a Afghanistan kawo ranar Juma'a tun bayan da Amurka ta kwashe Sojojinta daga kasar.

Wani masani kan lamarin ya bayyanawa Reuters cewa da yiwuwan Taliban ta kwace Kabul, babbar birnin kasar cikin kwanaki 30.

Wani jami'in gwamnatin Amurka wanda ya bukaci a sakaye sunasa ya bayyanawa Washington Post cewa "abubuwan na cigaba da tabarbarewa".

Nan da watanni uku, Taliban zata kwace babbar birnin Afghanistan gaba daya: Amurka
Nan da watanni uku, Taliban zata kwace babbar birnin Afghanistan gaba daya: Amurka Hoto: www.aljazeera.com
Asali: UGC

Bamu nadamar kwashe Sojojinmu, Amurka

Duk da haka, shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya ce bai nadamar kwashe Sojojin Amurka daga Afghanistan inda ya jaddada cewa wajibi ne Afghanistan ta taimaki kanta.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

Yace:

"Duba, mun kashe sama da Tiriliyan daya cikin shekaru 20. Mun horas, mun bada makaman zamani ga Sojin Afgahnistan sama da 300,000. Saboda haka shugabanninsu ya kamata su hada kai."
"Mun yi rashin dubban sojojin Amurka, da dama sun jikkata."

Rahoton cewa Taliban za ta kwace Kabul kwanan nan ya wuce tsammanin da akayi a baya.

A watan Yuni, rahoton leken asiri ya nuna cewa cikin watanni shida ake sa ran haka ya faru.

Gwamnan New York Ya Yi Murabus Kan Zargin Cin Zarafin Mata

A bangare guda, Gwamna Andrew Cuomo na jihar New York ta kasar Amurka, ya yi murabus daga mukaminsa bisa zargin da ake masa na neman mata.

Gwamnan ya sha matsin lamba daga mutane da dama na ya sauka da matsayin gwamna bayan wasu mata da dama sun zarge shi da cin zarafinsu.

Ya sanar da matakin murabus ɗinsa ne biyo bayan wani rahoto da ofishin Antoni Janar na jihar ya nuna zarginsa da cin zarafin mata a lokuta da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng