Da duminsa: Allah ya yiwa babban limamin Masallacin Quba rasuwa

Da duminsa: Allah ya yiwa babban limamin Masallacin Quba rasuwa

Babban limamin Masallacin Quba a kasar Saudiyya, Sheikh Muhammad Bin Abdallah Zarban Algamidy, ya rigamu gidan gaskiya.

Masallacin Quba a Saudiyya ne masallacin na farko da Annan Muhammad (SAW) ya fara ginawa yayin Hijrarsa daga Makkah zuwa Madina.

Manyan malaman Najeriya da sukayi karatu wajensa a Saudiya suka sanar da labarin mutuwarsa yayinda suke addu'a Allah yayi masa rahama.

Malami, Sheikh Jameel Muhammad Sadis, yace:

"Mun rasa Uba kuma babban masoyi. Allah ya gafarta ma Sheikh Muhammad Bin Abdallah Zarban Algamidy. Allah ya lullubeshi da rahamarsa."

Da duminsa: Allah ya yiwa babban limamin Masallacin Quba rasuwa
Da duminsa: Allah ya yiwa babban limamin Masallacin Quba rasuwa Hoto: Jameel Muhammad Sadis
Asali: Facebook

Khalifan marigayi Malam Albani Zaria, Sheikh Muhammad Auwal Maishago kuwa yace:

"Ash-Sheikh Zarban yana daga cikin manyan Malaman da Ash-Sheikh Albaniy Zaria (RH) yayi Karatu a hannunsu a Saudiyya ba a matsayin 'dalibin jami'a ba amma a matsayin shi na 'dalibi wanda ya kai kan shi Saudiyya don niman ilimi da koyon sa.
Haduwar su na 'karshe da Ash- Sheikh Albaniy Zaria har sai da yayi mishi raha yace mishi toh yanzu Albaniyn computer ne ko Albaniyn Hadisi? Sai Albaniy Zaria (RH) yace mishi Albaniyn duka ne. Sai Sheikh Zarbān (RH) yace mishi madalla da wannan laqabi, yace wannan laqabi ne wanda me shi bazai taba nadama ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel