Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yiwa yan sanda biyu yankan rago, sun bankawa ofishinsu wuta

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yiwa yan sanda biyu yankan rago, sun bankawa ofishinsu wuta

Umauka, jihar Imo - Hankulan jama'a sun tashi a garin Umuaka, karamar hukumar Njaba ta jihar Imo yayinda wasu yan bindiga suka banka wuta ofishin yan sandan Umuaka, rahoton Sun.

Rahoton ya kara da cewa sun kona barikin yan sandan kuma sun yiwa jami'an yan sanda biyu yankan rago.

Wannan hari ya auku ne da sanyin safiyar Asabar, 31 ga Yuli, 2021.

Amma wasu jami'an yan sanda da suka samu labarin aukuwan lamarin sun garzaya wajen inda suka hallaka yan bindigan biyu yayinda sauran suka arce.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya tabbatar da harin da kuma kisan yan bindigan biyu, amma bai tabbatar da kisan yan sanda biyu ba.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi yan sanda biyu yankan rago, sun bankawa ofishinsu wuta
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi yan sanda biyu yankan rago, sun bankawa ofishinsu wuta
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel