Labari Da Ɗuminsa: An Kawo Sunday Igboho Kotu a Kotonou

Labari Da Ɗuminsa: An Kawo Sunday Igboho Kotu a Kotonou

Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya isa Cour De’appal De Cotonou, wani kotu ta kasar Kotonou, Vanguard ta ruwaito.

Yan sandan kasa da kasa ne suka kama Igboho, mai rajin kare hakkin Yarbawa a kasar Kotonou.

Rahotanni sun bayyana cewa za a gurfanar da shi a kotun ne kan wasu laifuka masu alaka da saka dokokin hukumar shige da fice a cewar NewsWireNG.

Labari Da Ɗuminsa: An Kawo Sunday Igboho Kotu a Kotonou
Labari Da Ɗuminsa: An Kawo Sunday Igboho Kotu a Kotonou
Asali: Original

Yomi Alliyu (SAN), lauyan Igboho ya yi ikirarin cewa an kama Igboho da matarsa, Rapa, a hanyarsu na zuwa kasar Jamus.

Ya kuma yi ikirarin cewa ana azabtar da wanda ya ke karewa, yana mai cewa an daure masa hannu da kafa kamar dabba a wurin yan sanda.

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel