Litan Man Fetur zai koma N1000 idan aka cire tallafi, Hukumar DPR

Litan Man Fetur zai koma N1000 idan aka cire tallafi, Hukumar DPR

  • Hukumar DPR ta bayyana halin da yan Najeriya zasu shiga idan aka cire tallafin mai
  • A makonni biyu da suka gabata, majalisar dokokin tarayya ta zartar da dokar PIB
  • Wannan doka ta tayar da hatsaniya tsakanin yan majalisan kudu da Arewa

Hukumar arzikin man fetur DPR tace farashin litan man fetur a Najeriya ka iya tashi har N1000 idan aka cire tallafin man fetur ba tare da samo wata mafita ba.

Diraktan DPR, Sarki Auwalu, ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyi bayan jawabin da ya gabatar a liyafar cin abincin da yan kungiyar man fetur suka shirya a Legas, rahoton Punch.

Yayinda aka tambayesa shin me yasa ake samun sabanin adadin litan man fetur din da yan Najeriya ke sha kulli yaumin tsakanin hukumarsa da NNPC, Auwalu yace kudin da Najeriya ke kashewa kan tallafin mai ya yi yawa.

Yace idan za'a cire tallafin, to ya kamata a samarwa yan Najeriya wata mafita idan ba haka ba farashin mai zai yi tashin gwauron zabo.

Kara karanta wannan

Shugaban hafsan soji ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali zai magance tsaro

Litan Man Fetur zai koma N1000 idan aka cire tallafi, Hukumar DPR
Litan Man Fetur zai koma N1000 idan aka cire tallafi, Hukumar DPR
Asali: UGC

A cewar jawabin da hukumar ta daura kan shafinta ranar Litinin, Auwalu yace mafitar itace canza motoci zuwa masu amfani da iskar gas na girki LPG ko kuma CNG.

Yace duka-duka bai wuci a kashe $400 wajen canja mota daga man fetur zuwa gas ba.

A cewarsa:

"Saboda haka idan aka cire tallafi, abinda ake bukata shine mafita. Idan ba'a samo wata mafita ba, toh mutane zasu biya mai tsada."

"A yau akwai motoci milyan 22 a Najeriya. Ana amfani da motoci milyan takwas don haya."

"Muddin aka cire tallafi, man fetur ka iya komawa N1,000."

Asali: Legit.ng

Online view pixel