Sarkin Karaye ya dakatad da Dagacin da ya sayarwa Fulani Makiyaya fili

Sarkin Karaye ya dakatad da Dagacin da ya sayarwa Fulani Makiyaya fili

  • Filin da aka sayarwa Fulani na tayar da rikici a masarautar Karaye
  • Masarautar garin ta dauki matakin dakile matsalar
  • Sarkin Karaye ya nada wanda ya jagoranci al'ummar garin nanwucin gadi

Masarautar Karaye ta dakatad da Dagacin kauyen Butu-Butu, Abdullahi Sa'adu, na karamar hukumasr Rimingado, na jihar Kano, kan sayar da fili ga Fulani Makiyaya.

Karaye daya daga cikin Masarautun da gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkira ne a 2019.

Kakakin masarautar, Haruna Muhammad Gunduwawa, ya saki jawabin dakatar da dagacin ranar Juma'a, rahoton TheCable.

Jawabin yace:
"Fulani makiyaya sun gina Masallaci kan fili ba bisa ka'ida ba kuma hakan ya tayar da rikici a garin."
"An dakatad da shi ne domin kwamitin da aka kafa ta gudanar da bincike kan tuhumu-tuhumen da aka yiwa Dagacin."
"Dagacin Rimingado, Auwalu Ahmad Tukur (Magajin Rafin Karaye) da farko ya rubuta da takardar tuhuma ga Sarkin Karaye, Abubakar Ibrahim II kan abinda Dagacin yayi."

Kara karanta wannan

Najeriya ce ta 98 a jerin kasashe 107 da ke fama da yunwa a duniya

Sarkin Karaye ya dakatad da Dagacin da ya sayarwa Fulani Makiyaya fili
Sarkin Karaye ya dakatad da Dagacin da ya sayarwa Fulani Makiyaya fili Hoto: Kano State Gov't
Asali: Facebook

Bayan haka, Sarkin Karaye ya tura Madakin Shamaki, Habibu Umar, ya jagoranci lamuran garin gabanin kammala binciken.

Masarautar ta yi kira da al'ummar Butu-Butu sun hada kai da Madakin Shami wajen gudanar da ayyukansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng