Yanzu-yanzu: Wani abin fashewa ya tashi a cikin jihar Kaduna

Yanzu-yanzu: Wani abin fashewa ya tashi a cikin jihar Kaduna

Wani abin fashewa ya tashi a unguwar Badarawa dake jihar Kaduna kuma ya jikkata kananan yara masu wasa.

Daily Trust ta rahoto cewa wanda abu ya faru ne yayinda yaran ke wasa da wasu robobi.

An garzaya da yaran da suka jikkata asibiti.

Rahoton ya kara da cewa hannaye biyu na daya daga cikin yaran sun fille.

Wani mai idon shaida yace:

"Abin da ban takaici saboda daya daga cikinsu hannayensa sun fille, abin ya kuma shafin idonsa daya yayinda daya kuma ya jigata sosai."
"An ce wani mutumi ne ya basu goran BoBo suyi wasa.

Yanzu-yanzu: Wani abin fashewa ya tashi a cikin jihar Kaduna
Yanzu-yanzu: Wani abin fashewa ya tashi a cikin jihar Kaduna
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel