Shugaban Kamfanin BUA, AbdulSamad Isyaka Rabiu ya rabawa ma'aikatansa kyautan N2bn

Shugaban Kamfanin BUA, AbdulSamad Isyaka Rabiu ya rabawa ma'aikatansa kyautan N2bn

  • Bayan kyaututtukan da yake yiwa jami'o'i, ya tuna da ma'aikatan kamfaninsa
  • AbdulSamad Rabiu ya shahara da bada talaffi da kyauta
  • A farkon makon nan shugaban kasar Faransa ya bashi mukami

Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya sanar da rabawa ma'aikatansa kamfaninsa kudi naira bilyan biyu kyauta bisa kokarin da sukayi a shekarar 2020.

Kudin da ya basu wani yanki ne na hannun jarin da yake da shi domin kara musu karfin gwiwa saboda kamfanin ta samu riba a shekarar 2020 duk da annobar Korona.

A jawabin da ya fito daga ofishin Abdul Samad Rabiu, ya ce akwai muhimmanci ya nuna farin cikinsa ga ma'aikatan saboda kokarin da sukayi na tabbatar da cewa kamfanin ta samu cigaba da gindin zama.

A jawabin da Daily Nigerian ta samo, Rabiu yace:

Yayinda muke shiga sabuwar shekara, wannan kyauta da muka yiwa ma'aikatanmu shine abinda ya dace.
Bayan haka, ma'aikatanmu zasu sani cewa zasu amfana da nasarorin BUA gobe kuma hakan zai sa su cigaba da kokari.

Shugaban Kamfanin BUA
Shugaban Kamfanin BUA, AbdulSamad Isyaka Rabiu ya rabawa ma'aikatansa kyautan N2bn Hoto: BUA
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng