Daukar aiki: NDLEA ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara

Daukar aiki: NDLEA ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara

  • NDLEA ta fitar jerin sunayen wadanda suka yi nasarar daukar aikin da hukumar ta yi a shekarar 2019
  • Ana bukatar wadanda suka samu nasarar da su bayyana zuwa wurin tantance su a Jos kafin ranar 20 ga watan nan
  • Ya ce za a sake fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasarar har karo guda biyu nan gaba

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta fitar da jerin sunaye na karshe na wadanda suka yi nasara a daukar aikin da hukumar ke yi na shekarar 2019.

Babban daraktan hukumar kan hulda da da wayar da kan jama’a, Mista Femi Babafemi, shi ya bayyana haka a wani jawabin da ya fitar ranar Alhamis a Abuja kuma Legit ta samu.

Ya ce an fitar da jerin sunayen karshe na wadanda suka yi nasarar a mukamin na Narcotic Officer Cadre da rukunin farko na mukamin Narcotic Assistant cadre wadanda aka wallafa a shafin intanet na hukumar: www.ndlea.gov.ng

Ya kara da cewa wadanda suka yi nasarar ana bukatar su bayyana a Kwalejin hukumar NDLEA da ke Kotton Rikus a Jos tare da muhimman takardunsu.

NDLEA ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara
Daukar aiki: NDLEA ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara Hoto: NDLEA
Asali: Facebook

Takaddun sun hada da, takardun asali da kuma na kwafin takardun shaidarka da takardan shaidar neman aikin na NDLEA da mutum ya yi a intanet da hotunan fasfo guda hudu masu girman 5×7 masu kala kuma ba tare da hula ba da kayan rubutu kamar biro da fensir da litattafan rubutu da fayil, da dai sauransu.

Sannan ya bukaci dukkan wadanda suka yi nasarar da su kiyaye ka’idojin yaki da cutar COVID-19 a kowane lokaci, ya kara da cewa duk wanda ya kasa bayyana a wajen da misalin karfe 6.00 na yamma a ranar 20 ga Yuli, to kawai an cire shi a lissafi.

Ya ce za a fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasarar rukuni-rukuni.

Yace:

“Sunaye guda 1,000 na wadanda suka yi nasarar na babban mukamin shi ne rukuni na farko daga cikin rukuni guda uku da za a fitar. Ragowar rukunin guda biyu za a sake su ne a nan gaba,”

Asali: Legit.ng

Online view pixel