Cigaba: Mota mai tashi ta kammala shawagin gwaji na minti 35

Cigaba: Mota mai tashi ta kammala shawagin gwaji na minti 35

  • An yi gwajin shawagin motar musamman tsakanin tashar jirgin Nitra da Bratislava a ranar Litinin 28 ga Yuni
  • Motar mai shawagi tana amfani ne da injin din BMW sannan tana amfani da man fetur
  • An kera motar mai karfin daukar mutum masu nauyin kilogriram 200

Motar mai tashi, an kusan fara kera ire-irenta a wani muhimmin abin ci gaba bayan da ta yi shawagin gwaji na minti 35 tsakanin filayen tashin jiragen sama guda biyu.

Shawagin gwajin an gudanar da shi ne tsakanin tashoshin jiragen saman Nitra da na Bratislava – dukkansu na kasa-kasa a ranar Litinin 28 ga watan Yuni.

Mota mai tashi ta kammala shawagin gwaji na minti 35
Cigaba: Mota mai tashi ta kammala shawagin gwaji na minti 35 Hoto: Daily Hunt
Asali: Twitter

An saka mata injin din BMW

A cewar wani rahoton BBC, motar ta musamman an hada ta da injin din BMW ne sannan kuma tana amfani ne da man fetur.

Stefan Klein, shi ne wanda ya asssasa fikirar, ya ce za ta iya shawagin kimanin kilomita 1,000 sannan za ta iya tashi sama har tsawon kafa 8,200 kuma zuwa yanzu ta yi sa’o’i 40 a sararin samaniya.

Ya bayyana cewa yana daukar mintuna biyu da dakika 15 kafin a canza ta daga mota zuwa jirgin sama.

Kafin ta tashi sama, fuka-fukan nata tare da gefen motar za a lankwasa su. Klein ya tuka motar kai tsaye daga titin saukar jirgin zuwa cikin gari lokacin da ya isa yayin gwajin jirgin, wanda 'yan jaridar da aka gayyata suka shaida.

Ya bayyana lamarin a lokacin gwajin da aka yi a safiyar Litinin, 28 ga watan Yuni, a matsayin "abu da aka saba" kuma "mai dadi sosai".

A cikin sararin samaniya, motar ta yi gudun kilomita 170 a cikin sa’a guda.

Sabuwar kirar na wannan motar tana da karfin daukar mutum biyu masu nauyin kilogiram 200.

Tana bukatar titin jirgin sama kafin ta iya tashi sama, sai dai sabanin samfurin jiragen nan marasa matuki, ita wannan motar ba za ta iya tashi ta sauka a kaikaice ko ta mike santal kamar sanda ba dole sai tana bukatar titin jirgin sama.

Wannan sabuwar fasahar na zuwa ne lokacin da ake da matukar bukata da fata na kasuwar motoci masu tashi, wadanda aka dade ana jiran wanzuwarsu a matsayin makomar motoci a nan gaba.

A cikin 2019, wani kamfanin tuntuba mai suna Morgan Stanley ya yi hasashen cewa kasuwar motoci masu tashi zai iya kai wa N613 tiriliyan zuwa shekarar 2040.

Kuma a wani taron masana’antu a ranar Talata, 29 ga watan Yuni, shugaban kamfanin Hyundai Motors reshen nahiyar Turai Michael Cole ya kira lamarin da cewa “wani bangare ne na makomarmu”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel