Mambobin coci suka tunkari Fasto da fada saboda ya sayi sabuwar mota, sun ce ya mayar musu da kudaden zakkarsu
- Wani Fasto ya ga ta kansa bayan ya sauka daga sabuwar motarsa, kamar yadda bidiyo ya nuna
- A wani bidiyon da ya yi ta yawo fusatattun mabiya cocin sun tukari Faston da fada inda wadansu suka ci kwalarsa
- An samu ra’ayoyi masu cin karo da juna game da bidiyon inda mabiya cocin suke neman a biya su kudin zakkarsu
Da alama mallakar sabuwar mota da wani Fasto ya yi bai yi wa mabiya cocin nasa dadi ba.
Ana iya shaida bacin ran mabiyan ne ta cikin wani faifan bidiyon da ya karade shafukan intanet inda suke tunkarar Faston.
Wani bidiyon da wani mai amfani da sunan @kingtundeednut, ya dora a shafin Instagram ya nuno fusatattun mabiyan sun afkawa Faston inda wadansu suka ci kwalar rigarsa jim kadan bayan ya fito daga cikin sabuwar motar da ya saya mai launin fari kirar Range Rover.
Daga nan sai aka ji hayaniya ta barke yayin da mabiyan suka ci kwalar rigar Faston da ba a bayyana ko wane ne shi ba.
Bayanai sun nuna cewa mabiyan sun bukaci da lallai a mayar musu da kudaden da suka bayar a matsayin zakkar coci.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun bayyna ra’ayoyi masu cin karo da juna
Yayin da wadansu ’yan Najeriya suke jin cewa abin da mabiyan suka yi sam bai dace ba, wadansu kuma sun ce Allah Ya kara.
@yetundebakare ya rubuta:
"Abin lokaci ne kawai amma ba za su samu a mayar musu da kudaden nasu ba saboda ai zakkar coci ta Ubangiji ce."
@jnrpope ya bayyana cewa:
"Fastoci ma ba a bar su a baya ba….Lokacin da yunwa ta shigo, to mutane za su bukaci da mayar musu da kayan da suka mallaka."
@vjoofficial ya yi sharhi cewa:
"Kawai ku karbe kudadenku, kudaden da kuka bai wa Ubangiji ya wawure ya je ya sayi mota da su."
@domingo_loso ya ce:
"Wannan ai cin fuska ne, shin bindiga suka saka maka a ka kafin ka bayar da zakkar cocin ne. Sakarcinku ya kai inda ya kai lallai?"
@usherjeekk yana jin cewa:
"Wadansu mutane na tunanin ’yar Naira 50 din da suke bayar wa a matsayin kyauta ita ce za ta saya wa Fastonsu jirgin sama mai saukar ungulu. Galibin wadannan Fastocin suna rubuta littatafai kuma suna da harkokin kasuwanci."
Wata mata ta bayyana yadda Fastoci a dukkanin cocin da ta halarta suke neman ta da lalata.
A daya gefen kuma kafar labarai ta Legit.ng a kwanakin baya ta ruwaito wata ta bayyana yadda Fastoci a dukkanin majami’un da ta taba halarta suka neme ta da lalata.
A cewar matar mai suna Abena, yawancin Fastocin sukan hakaito kissar Annabi Ibrahim inda suka ce yana kwanciya da Hajar yayin da yake kuma auren Saratu, a matsayin hujjarsu ta neman ta da lalata.
Duk da yake ta rika bayyan musu cewa ita fa matar aure ce, amma sam Fastocin ba sa damuwa da wannan kawai abin da suke bukata daga gareta shi ne ta bayar da kai ga bukatarsu.
Matar wacce kwararriya ce a harkar bada shawarwari ga masoya ta ce akwai dimbin coci a kasar Ghana da suke da mata da dama wadanda sam ba sa damuwa su kwanta da Fastocinsu saboda sun yi amanna da hakan sosai.
Asali: Legit.ng