Ba zan dawo Najeriya ba sai na samu aminci kan tsaro da lafiyana, Ja'afar Ja'afar

Ba zan dawo Najeriya ba sai na samu aminci kan tsaro da lafiyana, Ja'afar Ja'afar

Dan Jarida kuma mai gidan jaridar DN, Ja'afar Ja'afar, ya arce daga Najeriya zuwa kasar Birtaniya bayan zargin tsegumi da bita da kullin da ake yi masa.

A hirar da Legit Hausa tayi da wani na kusa da Ja'afar ranar Litnin, ya bayyana cewa Ja'afar ya kwashe iyalansa zuwa Birtaniya kuma ba zai dawo ba sai ya samu aminci kan tsaronsa da lafiyarsa.

Yace, "Ya fada min cewa ba zai dawo yanzu ba. Ko bizarsa ta kare zai nemi mafaka wajen gwamnatin Birtaniya har zuwa lokacin da abubuwa sukayi sauki."

Ja'afar ya shiga wasar buya da gwamnati ne lokacin da hukumar yan sanda ta gayyacesa kan zargin batawa Sifeto Janar na yan sanda suna.

Daga nan sai dai aka samu labarin ya gudu Birtaniya.

Kimanin wata daya yanzu, gwamnna jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce wadanda suka kagi bidiyonsa yana karban daloli za su ji kunya.

Ba zan dawo Najeriya ba sai na samu aminci kan tsaro da lafiyana, Ja'afar Ja'afar
Ba zan dawo Najeriya ba sai na samu aminci kan tsaro da lafiyana, Ja'afar Ja'afar Hoto: PT
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel