Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana adadin mutanen da yan bindiga suka kashe a shekara daya

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana adadin mutanen da yan bindiga suka kashe a shekara daya

Gwamnatin jihar Kaduna a ranar Laraba ta bayyana adadin mutanen da yan bindiga suka sace da kuma adadin da suka kashe a jihar a shekarar 2020 da ta gabata.

A cewar rahoton da gwamnatin jihar ta saki, yan bindiga sun kashe mutum 937 a kananan hukumomin jihar 23, hakazalika an sace mutane 1,972.

A rahoton da ma'aikatar tsaron cikin gida ta saba fitarwa kowani shekara, yankin tsakiyar Kaduna ta debi kaso mafi yawa na adadin mutanen da aka hallaka.

Yayin gabatar da rahoton ga gwamnan Nasir El-Rufa'i na jihar, kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Giwa da Chikun, an kashe mutum 468.

"Mutane 286 aka hallaka a kudancin jihar, sakamakon rikice-rikice wanda tsageranci ya haifar musamman tsakanin Yuni da Nuwamba 2020," ya kara.

Kwamishanan ya kara da cewa cikin mutane 1,972 da aka sace a shekarar, 1,561 aka samu yankin tsakiyar Kaduna kuma 1,461 a kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Giwa da Chikun ne.

"Bayanan ya nuna cewa lallai tsageranci, garkuwa da mutane, satar shanu sun kasance manyan kalubale a jihar tare da rikice-rikicen kabilu." Aruwan ya kara.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana adadin mutanen da yan bindiga suka kashe a shekara daya
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana adadin mutanen da yan bindiga suka kashe a shekara daya Hoto: @GovKaduna
Source: Twitter

Source: Legit

Tags:
Online view pixel