Ku daina kiran yan bindiga da sunan masu laifi, kuma yan jarida masu laifi ne: Ahmad Gumi

Ku daina kiran yan bindiga da sunan masu laifi, kuma yan jarida masu laifi ne: Ahmad Gumi

Shahrarren Malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce yan jaridan Najeriya masu laifi ne saboda yawancin bada rahoton cewa yan bindigan Najeriya masu laifi ne kuma yan ta'addan ne.

Gumi, ya kasance kan gaba wajen tattaunawa da tsagerun yan bindiga a cikin daji domin sulhu da su.

A cewar Gumi, yan bindigan ba zasu mika wuya ba idan yan jarida suka cigaba da kiransu da sunan masu laifi.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a hirarsa da gidan talabijin Arise.

Ku daina kiran yan bindiga da sunan masu laifi, kuma yan jarida masu laifi ne: Ahmad Gumi
Ku daina kiran yan bindiga da sunan masu laifi, kuma yan jarida masu laifi ne: Ahmad Gumi Credit: Sheikh Ahmad Abubakar Gumi
Source: UGC

"Kuna ta nanata cewa masu laifi ne. Ai ko yan jaridan Najeriya masu laifi ne saboda suna karawa wuta mai. Wadannan mutanen na jin ku, ku daina kiransu masu laifi idan kuna son su mika wuya," Sheikh Gumi ya bayyana.

"Matasan shirye suke da ajiye makamansu, yanzu idan suka ji kuna kiransu da sunan masu laifi, ta yaya zasu bada hadin kai."

Saboda haka wajibi ne ku nuna musu su ma yan Najeriya ne kuma kada su cutar da yaranmu kuma su kasance masu bin doka, ire-iren wadannan kalaman muke son ji daga harsunan yan jaridar domin a samu a ceto yaran."

"Idan muka yi musu magana da kalamai masu dadi, shirye suke da ajiye makamai, shirye suke su sauraremu, amma idan ana kiransu masu laifi, ana kira ga kashesu, ko dauresu, ga irin halin da zamu shiga," Gumi ya kara.

Source: Legit.ng

Online view pixel