2021: Sanannun manya 10 da suka rasu a cikin watan Janairu

2021: Sanannun manya 10 da suka rasu a cikin watan Janairu

- Cikin watan Janairu na wannan shekarar 2021 an yi rashin wasu manya-manyan yan Najeriya sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 da wasu cututtukan daban

- Daga cikin manyan mutanen akwai mayan malamai, sarakunan gargajiy, 'yan siyasa da attajirai

1. Farfesa Ebere Onwudiwe

A ran 9 ga Janairu 9 Onwudiwe, farfesa na kimiyyar siyasa a Central State University, Wilberforce, Ohio, ya mutu sakamakon kamuwa da cutat COVID-19. Ya kasance sanannen masanin tattalin arziki, masanin kimiyyar siyasa, fitaccen marubuci.

2. Rear Admiral Ndubuisi Kanu (13 ga Janairu)

Kanu, tsohon administrator a zamanin mulkin soja a jihar Legas kuma memba na National Democratic Coalition (NADECO), sannan kuma mai rajin sake fasalin kasa da tafiyar da mulkin dimokiradiyya, ya rasu yana da shekara 77 bayan gajeriyar rashin lafiya a garinsu da ke Jihar Imo.

3. Prince Bolu Akin-Olugbade (Janairu 13)

Marigayi Prince Bolu Akin-Olugbade ya rike sarautar gargajiya ta Aare Ona-Kankanfo na Masarautar Owu. Ya kasance lauya kuma dan kasuwa, wanda ke da burin bunƙasa kadarori, gine-gine, kere-kere, kayan aiki, rarrabawa, ayyukan jiragen ruwa da na waje da bankin saka jari.

4. Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu (January 1)

Kafin rasuwarsa, Alhaji Bashir Aminu, babban mai fada a ji a masarautar Zazzau da ke Jihar Kaduna, ya shigar da gwamnatin jihar kara a kan nada Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau.

2021: Sanannun manya 10 da suka rasu a cikin watan Janairu
2021: Sanannun manya 10 da suka rasu a cikin watan Janairu
Source: Twitter

5. Dauda Birma (Janairu 5)

Alhaji Birma, tsohon ministan ilimi, ya kasance dan takarar shugaban kasa a karkashin rusasshiyar jam’iyyar ANPP. Ya mutu da sanyin safiyar Talata, 5 ga Janairun 2021 a gidansa da ke babban birnin jihar Adamawa, Yola.

6. Folake Aremu (3 ga Janairu)

A ranar 3 ga Janairu, masana'antar fina-finai ta Najeriya ta yi rashin wata tsohuwar jarumar Yarbawa, Folake Aremu, wanda aka fi sani da Orisabunmi. Ta mutu tana da shekara 60.

7. Farfesa Duro Ajeyalemi (6 ga Janairu)

Marigayi Farfesa Duro Ajeyalemi na Jami’ar Jihar Legas, wanda ya yi ritaya yana da shekara 70 a watan Nuwamba na shekarar 2020, ya kasance shugaban tsangayar Ilimin Ilimi da kuma magatakarda mai rejista na Hukumar Kula da Jarabawar ta Jami’ar (JUPEB).

8. Bala Bawa Ka’oje (19 ga Janairu)

Ka’oje, tsohon ministan wasanni kuma shugaban hukumar wasanni ta kasa, ya mutu yana da shekara 60.

9. Gambo Jimeta (Janairu 21)

Muhammadu Gambo Jimeta, tsohon Sufeto-Janar na ’Yan sanda (IGP), ya samu karin girma zuwa mukaddashin Mataimakin Sufeto-Janar (AIG) a 1982 kuma aka mayar da shi sashin binciken manyan laifuka, Alagbon Close, Legas. Ya zama Mataimakin Sufeto-Janar (DIG) a 1984. Ya gaji Etim Inyang a matsayin IGP a 1986 sannan Aliyu Attah ya gaje shi a 1990

10. Justice Abdulkadir Orire (26 ga Janairu)

Abdulkadir Orire, tsohon Grand Khadi na Jihar Kwara, an haife shi a 1934 a Obaninsunwa a Ilorin. Shine ya kasance mafi dadewa a aiki a babbar kotun shari'ar daukaka kara ta jihar Kwara, tsakanin 1975 da 1999.

11. Dr Abba Tor Masta II, Shehu na Dikwa (23 ga Janairu)

Shehun Dikwa a jihar Borno, Mai Martaba, Dakta Abba Tor Masta II, ya mutu da sanyin safiyar Asabar 23 ga Janairu, bayan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba. Shi ne na biyu a matsayi bayan Shehun Borno.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel