Kano: Alarammomi 1000 sun fara taron yi wa Buhari da Nigeria addu'o'i na musamman

Kano: Alarammomi 1000 sun fara taron yi wa Buhari da Nigeria addu'o'i na musamman

- Wasu Malamam addinin Musulunci su dubu daya sun yi taron gudanar da addu'o'i na musamman ga shugaban kasa, Muhamadu Buhari

- An wallafa hotunan Malaman yayin da suke zaune domin gudanar da addu'o'in a wani fili da basu ambata ba

- Za'a iya shaida fuskar Sheikh Aminu Daurawa da Abdulmumin Jibrin Kofa a wurin taron addu'o'in

Wasu Malaman addinin Musulunci a Jihar Kano sun fara taron gudanar da addu'o'i na musamman ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da kasa baki daya.

Jaridar Daily Trust ta wallafa hotunan Malaman yayin da suke zaune domin gudanar da addu'o'in a wani fili da basu ambaci wurin da ya ke ba a Kano.

Za'a iya gani tare da shaida fuskar tsohon shugaban hukumar HISBAH a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da tsohon dan majalisar Kiru da Bebeji a majalisar wakilai ta kasa, Abdulmmumin Kofa.

A ranar Lahadi ne tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfes Attahiru Jega, ya bayyana gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a matsayin ''babban abin takici."

Kano: Alarammomi 1000 sun fara taron yi wa Buhari da Nigeria addu'o'i na musamman
Kano: Alarammomi 1000 sun fara taron yi wa Buhari da Nigeria addu'o'i na musamman @Daily_trust
Source: Twitter

Kano: Alarammomi 1000 sun fara taron yi wa Buhari da Nigeria addu'o'i na musamman
Kano: Alarammomi 1000 sun fara taron yi wa Buhari da Nigeria addu'o'i na musamman
Source: Twitter

Kano: Alarammomi 1000 sun fara taron yi wa Buhari da Nigeria addu'o'i na musamman
Kano: Alarammomi 1000 sun fara taron yi wa Buhari da Nigeria addu'o'i na musamman
Source: Twitter

Yayin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust, Jega ya ce gwamnatin Buhari ''ta gaza fitar da yawancin 'yan Nigeria kunya", kamar yadda TheCable ta wallafa.

Farfesa Jega ya rike hukumar INEC daga shekarar 2010 zuwa 2015, shekarar da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya sha kaye a hannun Buhari.

Tsohon shugaban kungiyar ASUU da Jami'ar BUK da ke Kano, Farfesa Jega ya kasance shugaban INEC na farko, kuma daya tilo har yanzu, da ya fara gudanar da manyan zabuka guda; a 2011 da 2015.

A cewar Farfesa Jega, duk da har yanzu 'yan Nigeria na yi wa Buhari fatan alheri, 'yan kasa suna cikin damuwa ''akan alkiblar da kasa ke dauka."

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel