Kasar Rasha ta kaiwa Amurka mumunan hari, Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo

Kasar Rasha ta kaiwa Amurka mumunan hari, Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo

Sakataren wajen Amurka, Mike Pompeo ya daurawa kasar Rasha laifin harin yanar gizon aka kaiwa Amurka, wanda da masana sukayi siffanta matsayin mafi muni a tarihin Amurka.

Pompeo ne jami'in gwamnatin Trump na farko da ya bayyana cewa kasar Rasha ce tayi kokarin yiwa gwamnatin Amurka kutse ta yanar gizo.

Ana zargin Donald Trump da rashin magana kan lamarin da kuma kare dukiyoyin gwamnati ana saura wata daya ya sauka daga mulkin Amurka.

"Har yanzu muna binciken abinda ya faru, amma na sa za'a boye wasu bayanai," Pompeo ya bayyana a hira da Mark Levin.

"Amma akwai hujjan cewa an yi yunkurin amfani da manhajojin kutse shigar da wani wasu abubuwa na'urorin gwamnatin Amurka kuma an ga alama ya shafi na'urorin wasu kamfanoni masu zaman kansu da gwamnatoci a fadin duniya."

"Wannan babban yunkuri ne, kuma yanzu mun gani karara cewa yan kasan Rasha ne sukayi wannan abu."

Kasar Rasha ta kaiwa Amurka mumunan hari, Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo
Kasar Rasha ta kaiwa Amurka mumunan hari, Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo Photograph: Brendan Smialowski/AFP/Getty Images
Source: UGC

Har yanzu ba'a gano takamammen abinda masu kutsen ke nema ba, amma masana sunce zai iya hadawa da sirrukan makaman nukiliya, binciken rigakafin COVID-19, bayanai kan wasu manyan ma'aikatan gwamnatoci da sirrukan makamai.

Tuni dai Rasha ta ce ba ta da hannu cikin wannan kutse.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel