Yansandan Kano sun bankado ɓarayin salula, sun kwamushe 60, sun gano waya fiye da 100

Yansandan Kano sun bankado ɓarayin salula, sun kwamushe 60, sun gano waya fiye da 100

- Ana yawan samun rahotannin yadda batagarin matasa ke kwacen wayoyin bayin Allah a Kano

- Rundunar 'yan sandan Kano ta tashi tsaye wajen yaki da matsalar gadan-gadan

- Kwamishinan 'yan sandan Kano ya ce na'urar da gwamna Ganduje ya siyawa rundunar ta na matukar taimakawa a bangaren tsaro

Ƴansanda a Kano sun shiga farautar ɓarayin waya wanda hakan yayi sanadiyyar damƙe har guda sittin 60 daga cikinsu, ka na kuma sun gano ɗaruruwan wayoyin da ƴan daba suka kwata daga hannun bayin Allh ta ƙarfin tsiya.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, C.P Habu A.Sani, wanda akafi sani da "Kalamu Wahid" shine ya sanar da hakan lokacin taron ilmantarwa da masu sana'ar sayar da waya, inda akayi musu ƙarin haske akan buƙatar haɗa hannu da jami'an tsaro don yaƙar mummunar ta'adar ƙwacen waya.

Da yake nuna godiyarsa, kwamishinan ya ce; "nau'urar bin diddigi ta miliyan ₦500 da gwamnatin mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta siyawa rundunar 'yan sanda a Kano ya taimaka matuƙa wajen gano ɓarayin da kuma wayoyin da suka sace.

"Na'urar bin diddigin jami'an tsaron wadda ba iya mu kaɗai muke mora ba harda maƙwabtan jihohin Katsina, Jigawa, Zamfara, Sokoto da sauransu ta taimaka wajen yaƙar Fashi da makami, ta'addanci, satar mutane da sauran manyan miyagun laifuka" a cewarsa.

Yansandan Kano sun bankado ɓarayin salula, sun kwamushe 60, sun gano waya fiye da 100
CP Habu Sani @Vanguard
Asali: Twitter

Kwamishina Sani(Kalamu Wahid),wanda mataimakin Kwamishina mai kula da atisayen rundunar ya wakilta,DCP Balarabe Sule,yace

"Yawan samun koke koken mutane a Ɗan Agundi,Titin Obasanjo,Rijiyar Lemo,shine ya jawo hankali hukumar ƴansandan suka ɗauki matakin gaggawa inda su farwa ƴan fashin wayar ba ƙaƙƙautawa.

Legit.ng ta rawaito rundunar soji na cewa karfin soji kadai ba zai kawo karshen kalubalen tsaro da yankin arewa maso yamma da sauran sassan kasa ke fama da shi ba, tare da sanar da cewa "hatta a tsakanin sojoji akwai cin amana".

An fadi hakan ne yayin wani taro da rundunar soji ta yi da manema labarai daga Katsina da Zamfara wanda aka yi a sansanin soji na musamman da ke Faskari a jihar Katsina.

Rundunar sojin ta jaddada muhimmancin hada karfi da karfe a tsakanin hukumomin tsaro da sauran jama'ar farar hula domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: