Shugaba Buhari ya yi ta'aziyyar mutuwar Igwe Alex Nwokedi

Shugaba Buhari ya yi ta'aziyyar mutuwar Igwe Alex Nwokedi

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar rasuwar Igwe Alex Nwokedi, Uthoko na Achalla

- Marigayi Igwe Alex Nwokedi shine basaraken garin Achalla da ke jihar Anambra kuma ya rike mukamai da dama kafin rasuwarsa

- Shugaban kasar ya yi addu'ar Allah ya gafarta wa marigayin ya kuma bawa iyalansa da sauran wadanda ya bari hakurin jure rashinsa

Shugaba Muhammad Buhari ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan gidan sarautan Uthoko Na Eze bisa rasuwar Igwe Alex Nwokedi, Uthoko na Achalla.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya isa da sakon cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Buhari ya kuma yi wa al'ummar Achalla da majalisar Igwe na Achalla da gwamnatin jihar Anambra ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar Igwe Alex Nwokedi
Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar Igwe Alex Nwokedi. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kashe 'yan sintiri hudu da wasu yayin da 'yan bindiga suka kai hari a Katsina

Mr Nwokedi shine tsohon shugaban Majalisar Masu Sarautun Gargajiya na Jihar Anambra kuma tsohon shugaban Majalisar Masu Sarautun Gargajiya na Jihohin Kudu guda tara.

Ya kuma rike mukamin Manaja, Na sashin hulda da Jama'a ta NNPC kuma shine sakataren watsa labarai na Janar Olusegun Obasanjo a lokacin yana shugaban kasa na mulkin soja daga 1967 zuwa 1979.

KU KARANTA: Hotuna: An kashe 'yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji - DHQ

Shugaba Buhari ya ce Igwe Nwokedi ya aikata muhimman abubuwa da tarihi ba za ta manta da shi ba ya kuma yi adduar Allah ya gafarta masa ya kuma bawa wadanda ya bari a baya hakurin jure rashinsa.

A wani labarin, kun ji an cigaba da zanga-zanga, ranar Juma'a, a wasu ƙasashen Musulmi don nuna fushi kan kalaman shugaban Faransa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

An cigaba da zanga-zanga bayan sallar Juma'a a wurare daban-daban a zirin Gaza inda kungiyar Hamas ta bukaci masu zanga-zangar su hadu a sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia don cigaba da nuna fushin su kan batun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164