Kawai ka sauka daga mulki, ka gaza - Sarkin Calabar ga gwamnan Cross River

Kawai ka sauka daga mulki, ka gaza - Sarkin Calabar ga gwamnan Cross River

- Irin ta Kano, Sarkin gargajiyan jihar Cross River ya yi fito-na-fito da gwamnan

- Ya ce gwamnan ya daina daukar wayansa kuma ba ya kiransa

- Ya zargi gwamnan da rashin iya mulki da gudanar da al'ummar

Mai Martaba Obong na Calabar, Edidem Ekpo Okon Abasi Otu, ya daura laifin sace-sace da fashe-fashen da akayi a jihar Cross River makon da ya gabata kan gwamna Ben Ayade, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi kira ga gwamnan ya sauka daga mulki domin baiwa gwamnatin rikon kwarya daman gyara kuma ya natsu ya dauki darasin yadda ake mulki da tafiyar da al'umma.

Sarkin wanda yayi jawabin lokacin da ya karbi bakuncin tsohon gwamnan jihar, Liyel Imoke, ya ce an kai hare-haren ne saboda gwamnan ya daina shirya zaman hukumomin tsaro.

"Ya daina shirya zaman hukumomin tsaro. Da ya kira jami'an tsaro, ya zauna da su bayan samun labarin abinda ya faru a Legas da wasu wurare, da hakan bai faru ba, " yace.

Sarkin ya ce gwamna Ayade ba ya daukan wayansa idan ya kirashi.

Ya yi kira da gwamna ya canza dabi'unsa saboda kowani mai ruwa da tsaki a jihar na da hakkin ganin shugabansu.

Sarkin gargajiyan ya bayyanawa tsohon gwamnan cewa ya fadawa Ayade jihar ba zata cigaba ba idan ya cigaba da mulki haka.

"Mu fadi gaskiya, mu daina boye-boye; ba za mu iya cigaba da rayuwa haka ba. Ka fada mai akwai bukatar sulhu," ya ce.

Kawai ka sauka daga mulki, ka gaza - Sarkin Calabar ga gwamnan Cross River
Kawai ka sauka daga mulki, ka gaza - Sarkin Calabar ga gwamnan Cross River Credit: @senatorbenayade
Asali: Twitter

Amma daya daga cikin masu magana da yawun gwamnan, Christian Ita, ya ce gaskiya da kamar wuya a ce maigidansa yaki daukan wayar Sarkin.

Ya ce gwamnan na ganin girman Obong sosai a matsayinsa na uban kowa a jihar.

"Bai dace yayi kira ga gwamnan wanda yake iyakan kokarinsa wajen kawo cigaba jihar yayi murabus ba," yace.

A bangare guda, a wajen bikin cika shekaru 50 da kafa Arewa House da ke Kaduna, Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya karrama mutumin da ya tuka, Firimiyan Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello.

Sultan ya bukaci manyan baki da masu ruwa da tsaki da suka halarci taron da su karrama Alhaji Ali Sarkin Mota, sannan dattijon ya dunga bin wuri-wuri a dakin taron domin gaisawa da manyan mutane da taimakon sandar da yake dogarawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel