Gwamna Abdullahi Ganduje ne jagoran yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya - Dawisu
-Duk da zargin rashawa da ake yiwa Ganduje, hadiminsa ya ce shine jagaban yaki da rashawa a Najeriya
- Bayan makonni biyu, Ganduje ya dawo da Salihu Yakassai cikin gwamnatinsa
- Dawisu ya kafa hujjoji uku na lakabawa Ganduje jagoran yaki da rashawa
Mai bada shawara ga gwamna Ganduje kan kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, wanda aka fi sani da Dawisu ya bayyana cewa maigidansa ne jagoran yaki da rashawa a Najeriya.
A hirar da yayi da jaridar Aminiya, Dawisu ya bayyana dalilai uku da yasa ya fadi hakan.
Wannan ba shi bane karo na farko da ma'aikatan gwamnatin Ganduje zasu yi ikirarin fin kowace jiha a fadin tarayya yaki da cin hanci da rashawa.
Dawisu ya ce Ganduje ba ya yiwa hukumar shisshigi ko katsalandan a harkokinta, yana barinta tayi aikinta.
Zaku tuna cewa a shekarar 2018, wani faifan bidiyo ya nuna yadda gwamnan jihar Ganduje ke cusa daloli cikin aljihunsa.
Jaridar Daily Nigerian ta ce kudin rashawan kwangila ne gwamnan ya karba.
DUBA NAN: Gobara ta lashe dakin kwanan kwalejin horon malaman jinya ta Kano

Asali: Twitter
KU DUBA: Tallafin Korona: Mun yi asarar N75bn sakamakon sace-sacen da aka yi - Gwamnan jihar Plateau, Lalong
Dawisu yace: “Na farko dai, Kano ita ce jiha daya tilo da ke da hukuma mai zaman kanta da ke yaki da cin hanci da rashawa a duk fadin Nijeriya, kamar yadda ake da hukumar EFCC a matakin kasa."
“A nan ne talakawa ke kai kokensu a kuma bibiyi korafe-kirefensu a kwato musu hakkokinsu."
“Na biyu, hukumar ta samu nasarori da daman gaske, a kwana-kwanan nan; idan ba a manta ba lokacin coronavirus da ’yan kasuwa suka kara kudin kayan abinci, hukumar ce ta shige gaba aka sauko da farashin shinkafa – wannan ma nasara ce da ba a taba samun irin ta ba a kasar nan.
“Uwa uba ma ko jami’an gwamnati tsoro suke su yi wani abu na rashin gaskiya saboda hukumar ba za ta bari ba.
“Ta uku ita ce, ban da ita kanta hukumar, yanzu haka an samar da makarantar horar da ma’aikatanta kan dabarun yaki da cin hanci da rashawa sabanin a baya da sai dai a kai ma’aikatan horo Abuja”, inji shi.
Ya kara da cewa hukumar yaki da rashawar jihar ce ta bankadao badakalar tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
A bangare guda, gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo da Salihu Tanko Yakassai, wanda aka fi sani da Dawisu, bakin aikinsa na babban hadiminsa na kafafen yada labarai.
Ganduje ya yi hakan ne makonni biyu bayan dakatad da shi daga mukaminsa kan sukan shugaba Muhammadu Buhari da yayi a shafinsa na Tuwita
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng