Gobara ta lashe dakin kwanan kwalejin horon malaman jinya ta Kano

Gobara ta lashe dakin kwanan kwalejin horon malaman jinya ta Kano

- Annobar gobara ta aukawa daya daga makarantun gaba da sakandaren jihar Kano

- Yayin tattara wannan rahoto, ba'a sani ko gobarar ta raunata wasu ba

- Kwalejin wacce ke garin Madobi tana horon dalibai wajen ilimin jinya da unguzoma

Akalla dakuna 16 a gidan daliban kwalegin horon malaman jinya da unguzoma ta jihar Kano sun kone kurmus sakamakon gobara.

An ce gobarar ta fara ci ne lokacin Sallar Magariba misalin karfe 6:20 a ranar Laraba a tsauni na uku da dakin kwanan Sa'idu Fagge.

An tattaro cewa wutan ta samo asali ne daga ban daki.

Wata majiya a kwalejin ta bayyanawa The Punch cewa sai da aka kwashe awa daya ana gobararn kafin jami'an kwana-kwana suka iso.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Sa'idu Muhammad, ya tabbatar da aukuwan lamarin.

Ya ce an kaddamar da bincike domin gano abinda ya haddasa gobarar da kuma irin asarar dukiyan da akayi.

Gobara ta lashe dakin kwanan kwalejin horon malaman jinya ta Kano
Gobara ta lashe dakin kwanan kwalejin horon malaman jinya ta Kano Hoto: Kano State College of Nursing & Midwifery
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kuma dai: Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun halaka mutum 4

A bangare guda, mai bada shawara ga gwamna Ganduje kan kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, wanda aka fi sani da Dawisu ya bayyana cewa maigidansa ne jagoran yaki da rashawa a Najeriya.

A hirar da yayi da jaridar Aminiya, Dawisu ya bayyana dalilai uku da yasa ya fadi hakan. Wannan ba shi bane karo na farko da ma'aikatan gwamnatin Ganduje zasu yi ikirarin fin kowace jiha a fadin tarayya yaki da cin hanci da rashawa.

Dawisu ya ce Ganduje ba ya yiwa hukumar shisshigi ko katsalandan a harkokinta, yana barinta tayi aikinta.

KU DUBA: An saki ranakun buga wasar fiddan gwanin gasar AFCON tsakanin Najeriya da Sierra Leone

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng