Tallafin Korona: Mun yi asarar N75bn sakamakon sace-sacen da aka yi - Gwamnan jihar Plateau, Lalong

Tallafin Korona: Mun yi asarar N75bn sakamakon sace-sacen da aka yi - Gwamnan jihar Plateau, Lalong

- Jihar Plateau na daya daga jihohin da matasa sukayi wawasan kayan tallafin Korona

- Wasu bata gari sun yi amfani da hakan wajen fasa shagunan mutane sukayi sata

- Gwamnan jihar ya sassauta dokar hana fitan da ya sa karshen makon da ya gabata

Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong, a ranar Juma'a ta yi asarar bilyan 75 a sace-sacen da aka yi ranar Asabar da Lahadi sakamakon zanga-zangar #EndSARS.

Legit Hausa ta ruwaito yadda mazauna jihar suka fasa rumbunan abinci domin neman kayan tallafin Korona, amma wasu suka koma satan kayayyakin mutane.

Jami'an rundunar Operation Safe Haven sun damke sama da mutane 100 da ake zargi na wannan lalatan.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a hira da matasan jihar kan abubuwan da suka fari a gidan gwamnatin jihar dake Rayfield Jos.

Lalong yace: "Rahotannin da na samu daga masana shine abubuwan da akayi asara zasu kai bilyan 75 a yanzu."

"Wannan ci baya ne sosai saboda bamu da kudin maye abubuwan da aka lalata ko aka sace."

"Har yanzu bamu farfado daga illan da cutar COVID-19 tayi mana ba."

"Mun kirga dukiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu 32 da aka kaiwa hari akayi sace-sace."

KU DUBA: Kuma dai: Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun halaka mutum 4

Gwamnan ya kara da cewa ya san halin da matasan jihar ke ciki na rashin aikin yi da rayuwa mai dadi.

Ya yi kira ga matasan su guji yin duk wani abu da zai zama barazana ga zaman lafiya a jihar da Najeriya gaba daya.

Tallafin Korona: Mun yi asarar N75bn sakamakon sace-sacen da aka yi - Gwamnan jihar Plateau, Lalong
Tallafin Korona: Mun yi asarar N75bn sakamakon sace-sacen da aka yi - Gwamnan jihar Plateau, Lalong Hoto: @Asovilla
Asali: Facebook

DUBA NAN: Shahrarren da kwallon duniya, Cristiano Ronaldo, ya warke daga cutar Coronavirus

A wani labarin, a yunkurinsa na rage rashin aikin yi a jihar Legas, gwamna Babajide Sanwo-Olu ya kirkiro tsarin da zai rage yawan marasa aikin-yi.

Gwamnatin Legas ta skawo tsarin da ake kira Graduates Internship Placement Programme (GIPP) wanda zai yi maganin zaman banza.

A wannan sabon shiri, za a horas da masu zaman kashe wando, a koya masu sana’o’Ii kamar yadda gwamnatin jihar Legas ta bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel