Duka ba kama suna: Hadimin Ganduje, Yakasai, ya sake caccakar mahukunta bayan mayar da shi kujerarsa

Duka ba kama suna: Hadimin Ganduje, Yakasai, ya sake caccakar mahukunta bayan mayar da shi kujerarsa

- Salihu Tanko Yakasai (Ɗawisu), haɗimin gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya sake caccakar wadanda nauyin samar da tsaro ya rataya a kansu a Najeriya

- Ɗawisu ya ce babban nauyin da ya rataya kan ko wace gwamnati shine tsare rayuka da dukiyoyin al'ummar ta idan ba a samu hakan ba gwamnatin 'ta gaza'

- Tanko Yakasai ya faɗi hakan ne yayin martani kan harin baya-bayan nan da ƴan bindiga suka kai Zamfara

Salihu Tanko Yakasai, mashawarci na musamman kan kafafen watsa labarai na Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya sake sukar mahukunta a Najeriya kan gazawarsu wurin kare 'yan kasar daga harin ƴan bindiga.

Mista Yakasai ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter yayin da ya ke martani kan sabon harin da ƴan bindiga suka kai Zamfara idan suka kashe mutane da ba a faɗi adadi ba.

A rahoton da ta wallafa a ranar Juma'a 30 ga watan Oktoba, jaridar Daily Nigerian ta alakanta wannan sukar da Yakasai ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari.

Kakakin Ganduje, Dawisu ya sake yin magana a kan tsaro
Salihu Tanko Yakasai. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Duk da cewa Yakasai bai ambaci suna Shugaba Buhari ba a rubutun, ya ɗora laifin kan wadda hakkin samar da tsaro ya rataya a kansa duba da cewa samar da tsaron na kan gaba cikin ayyukan shugaban ƙasa a kundin tsarin mulki.

Ya ce: "Yadda ake rasa rayyuka ba tare da ganin alamun zuwan ƙarshen lamarin ba abu ne mai karya zuciya da tada hankali.

KU KARANTA: Zulum ya bayyana matakin da zai dauka kan ɓata garin da aka yi haya don yin zanga zanga a Borno

"Ɗauyin na farko da ya rataya a kan kowacce gwamnati shine tsare rayuka da dukiyoyi, idan ba a samu hakan ba, ka san cewa ka gaza."

DUBA WANNAN: 'Farautar 'yan bindiga suke yi' - Gwamnatin Kaduna ta yi karin haske kan jiragen sojoji da ke shawagi a jihar

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya, Gwamna Ganduje ya dakatar da Yakasai kan sukar Shugaba Muhammad Buhari da ya yi na cewa 'bashi da tausayi'.

Ya ƙara da cewa shugaban ƙasar baya yana ganin tamkar alfarma ya ke yi wa ƴan kasar idan ya yi musu jawabi kan abubuwan da ke damunsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel