Kuma dai: Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun halaka mutum 4

Kuma dai: Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun halaka mutum 4

- Bayan kisan mutane 20 a kimanin makonni 2 da suka shude, yan bindgia sun sake kai hari Zamfara

- Wannan karon karamar hukumar gwamnan jihar suka kaiwa farmaki

- An yi rashin akalla rayuka 4 yayinda akalla mutane 3 sun jigata

Wasu yan bindiga a ranar Alhamis sun kai hari garin Gidan Goga dake karamar Maradun na jihar Zamfara, inda mutane akalla hudu suka rasa rayukansu

Mazauna sun bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun dira garin kan babura suna harbin mutane kafin sukayi awon gaba da shanu da awaki.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya tabbatar da hakan ga manema labarai inda yace harin ya faru ranar Alhamis.

Wani tsohon kwamishanan ilimin jihar Zamfara, wanda dan gari Gidan Goga ne, Ibrahim Danmalikin Gidan Goga, ya bayyanawa Daily Trust cewa yan bindigan sun dira garin misalin karfe 1 na rana.

A cewar Shehu, ana samun rahoton aka tura jami'an yan sanda karkashin jagorancin DPO na Maradun domin kawar da yan bindigan da kuma hanasu karasawa wasu kauyukan, rahoton tashar Channels.

"Yan bindigan sun gudu kafin isar jami'an tsaro. Mutane hudu suka kashe yayinda 3 sun jigata. Yanzu haka suna jinya a asibitin FMC Gusau, " cewar Kakakin.

Ya kara da cewa yanzu an kara yawan jami'an tsaro a kauyen.

KU KARANTA: Bai Kamata Minista Sadiyya Ta Yaudari 'Yan Najeriya Ba - Panandas

Kuma dai: Yan bindiga sun kai mumunan hari jihar Zamfara, sunyi aika-aika
Kuma dai: Yan bindiga sun kai mumunan hari jihar Zamfara, sunyi aika-aika Credit: @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zulum ya bayyana matakin da zai dauka kan ɓata garin da aka yi haya don yin zanga zanga a Borno

A wani labarin daban, wani jami'in tsaro, jami'an sintiri hudu da wasu mutane da ba a san adadin su ba sun rasa rayukansu ranar Alhamis yayin da yan bindiga suka kai hari a kauyen Diskiru karamar hukumar Dandume a Jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun kai kimanin sama da 200 da makamai irin su AK-47, sun yi dirar mikiya a kauyen ranar Laraba da dare a abin da akace ramuwar gayya ce.

Sun kuma dinga kashe mutane har safiyar Alhamis, kuma a wannan lokacin sun kashe mutane da ba a san adadin su ba tare da yin garkuwa da yan mata da dama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng