An kashe 'yan sintiri hudu da wasu yayin da 'yan bindiga suka kai hari a Katsina

An kashe 'yan sintiri hudu da wasu yayin da 'yan bindiga suka kai hari a Katsina

- An kashe yan bindigar da ba a san adadin su ba yayin da jami'an tsaro suka kai hari kan yan bindiga

- Yan bindiga sun yi dirar mikiya kauyen Diskiru don yin ramuwar gayya kan kisan yan uwansu

- Yan bindigar sunyi garkuwa da yan mata da dama tare da kashe wasu da ba a san adadin su ba

An kashe jami'an sintiri hudu, da wasu mutanen harin yan bindiga a Katsina

Wani jami'in tsaro, jami'an sintiri hudu da wasu mutane da ba a san adadin su ba sun rasa rayukansu ranar Alhamis yayin da yan bindiga suka kai hari a kauyen Diskiru karamar hukumar Dandume a Jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun kai kimanin sama da 200 da makamai irin su AK-47, sun yi dirar mikiya a kauyen ranar Laraba da dare a abin da akace ramuwar gayya ce.

Sun kuma dinga kashe mutane har safiyar Alhamis, kuma a wannan lokacin sun kashe mutane da ba a san adadin su ba tare da yin garkuwa da yan mata da dama.

Yan bindigar sun kai harin ne don rama kisan wasu mutanen su guda uku da akayi satin daya gabata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Bincike ya bayyana cewa saboda lalacewar hanyar da zata kai ka kauyen, yan bindigar sun ci karen su babu babbaka kafin daga bisani jami'an tsaron da suka hada da yan sanda, Sojoji da jami'an Sintirin yankin su isa inda suke.

An kashe 'yan sintiri hudu da wasu yayin da 'yan bindiga suka kai hari a Katsina
An kashe 'yan sintiri hudu da wasu yayin da 'yan bindiga suka kai hari a Katsina. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Farautar 'yan bindiga suke yi' - Gwamnatin Kaduna ta yi karin haske kan jiragen sojoji da ke shawagi a jihar

Jami'an tsaron sun kai hari kan yan bindigar a wani shingen Makiyaya a Faskari, wanda hakan ya janyo musayar wutar da yayi sanadiyar mutane biyar.

An ruwaito cewa rundunar Sojojin sama na daga cikin hukumomin da suka taimaka wajen yakar yan tada kayar bayan, wanda ke barazanar mamaye dajin.

Mai magana da yawun rundunar yan sandar Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa suna ci gaba da bincike don gano yawan yan bindigar da aka kashe.

KU KARANTA: Kwamishina ya zubda hawaye bayan ganin 'satar' da 'yan daba suka yi a Kogi (Bidiyo)

"Lamarin ya faru a kauyen Diskiru karamar hukumar Dandume kuma yan bindigar sun zo ramuwar gayya ne. An kashe da yawan su yayin da Sojojin Sama dana Kasa suka kai musu hari. Bazan iya ce muku ga Adadin da aka kashe ba saboda har yanzu muna gudanar da bincike, amma dai an kashe jami'in tsaro da wasu jami'an sintiri hudu yayin da suke kokarin dakatar da maharan," a cewarsa

A wani labarin, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa makiyan kasar nan suka lalata zanga zangar #endsars da nufin rushe kasar.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata, 27 ga Oktoba a yayin tattaunawa da manema labarai kan yadda za a tabbatar da hadin kan Najeriya, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel