Bai Kamata Minista Sadiyya Ta Yaudari 'Yan Najeriya Ba - Panandas

Bai Kamata Minista Sadiyya Ta Yaudari 'Yan Najeriya Ba - Panandas

- Panandas ya yi tsokaci kan ikirarin Ministar Jin kai kan kayan abincin da ake wawashewa

- Hajiya Sadiya tuni ta bayyana cewa Allah ya wanketa daga zarge-zargen da ake mata

- Hakazalika ta ce ta yafewa dukkan wadanda sukayi mata kazafi

Matashi kuma Shugaban Kungiyar Masoya Buhari, Alhaji Mustapha Salisu Panandas ya caccaki Ministar Ma 'aikatar Jinkai da Cigaban Al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq bisa abinda ya kira yaudarar 'yan Najeriya da ta yi akan maganar rabon tallafin kayan abinci a fadin kasar nan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya daura mata alhakin rabawa al'ummar Najeriya.

Panandas wanda ya fadi haka a lokacin da yake zantawa da gidan rediyon Muryar Amurka, ya ce ministar ta ba shi kunya, sannan ta tonawa kanta asiri, inda ta bayyana cewa wai Allah Ya wanke ta, domin ta baiwa gwamnoni kayan tallafin amma ba su raba ba, sai da fusattun matasa suka riqa balle ma'ajiyar suna wawashe abincin.

"Bai kamata ministar ta yaudari 'yan Najeriya ba, saboda wadannan kayayyaki ba su da alaqa da kayan gwamnati kamar yadda Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ya fada, sannan su ma gwamnonin sun fada cewa ba na gwamnatin tarayya ba ne, amma ita saboda son banza da rinton zunubi ta ce ita ta raba kayan, wai Allah Ya wanke ta. Ina kuwa Allah Ya wanke ki? Gaskiya dai ta bayyana." Inji shi.

"Idan aka lura za a ga wadannan kayayyakin suna dauke da da samfurin 'CA COVID' ma'ana; Coalition against COVID-19, wadda yake nuna cewa kayayyakin da 'yan kasuwa irinsu Dangote, Abdulsamad, TY Danjuma, Jim Obia da sauransu suka saya ne, amma a rana saka ministar ta ce ita ta raba wadannan kaya."

"Kuma irin wannan matar ma bai kamata ace tana minista a qasa irin Najeriya ba, domin ba ta da qwarewar aiki, saboda ba wannan ne karon farko ba, a baya ma an sha samunta da irin wannan cogen," ya kara.

Bai Kamata Minista Sadiyya Ta Yaudari 'Yan Najeriya Ba - Panandas
Bai Kamata Minista Sadiyya Ta Yaudari 'Yan Najeriya Ba - Panandas Credit: Panandas
Asali: UGC

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne ministar ta Jin Kai ta kare kanta kan batun kayan tallafi da ta ce ta raba wa jihohi domin raba wa al'umma, inda ta fada wa BBC cewa ta sauke nauyin da aka dora mata bayan zarginta a baya da aka dinga yi kan kayan tallafi kafin wawason da wasu suka yi a rumbunan kayan abinci a jihohin kasar.

Hajiya Sadiya Farouq ta ce sun bai wa gwamnonin jihohi umarnin rarraba kayan tun a lokacin da suka kai musu.

"Mu dai mun sauke nauyin da ke kanmu, shugaban kasa ya ba mu kayan abinci kuma mun kai wa gwamnonin jihohi," a cewar Sadiyar Farouk.

"Ni dai ina aiki ne tsakani da Allah domin sauke amanar da aka daura mani kuma da ma ina cewa gaskiya za ta fito. To Alhamdulillahi," inji ta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel