Bidiyo: Galibin matasan Najeriya 'yan ƙwaya ne - Ƴar Majalisar Legas

Bidiyo: Galibin matasan Najeriya 'yan ƙwaya ne - Ƴar Majalisar Legas

- Ƴar majalisar Jihar Legas Mojisola Alli-Macaulay ta ce galibin matasan Najeriya a buge da ƙwaya suke a kullum

- Alli-Macaulay ta furta hakan ne a zauren Majalisar Jihar Legas yayin tattaunawa kan ɓarnar da aka yi sakamakon zanga-zangar EndSARs

- Ƴar majalisar ta kuma ce rashin ayyukan yi ba hujja bace ga matasa su zama ɓata gari inda ta shawarcesu su rungumi sana'ar hannu

Ƴar majalisar mai wakiltar mazaɓar Amuwo Odofin ta 1 a Jihar Legas, Mojisola Alli-Macaulay ta ce mafi yawancin matasan Najeriya cikin mayen ƙwayoyi suke a kullum.

Alli-Macaulay ta bayyana hakan ne yayin zaman majalisar jihar Legas da aka yi kan sata da ɓarna da ɓata gari suka yi sakamakon zanga-zangar EndSARs a cewar rahoton The Punch.

Galibin matasan Najeriya 'yan kwaya ne - Yar Majalisar Legas
Galibin matasan Najeriya 'yan kwaya ne - Yar Majalisar Legas. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Ƴar majalisar ta ce, "Ya kamata hukumar wayar da kai na ƙasa ta duƙufa wurin aiki. Akwai buƙatar mu fara wayar da kan matasan mu.

"Suna buƙatar mutanen da za su rika musu magana lokaci zuwa lokaci. Mafi yawancinsu tatil suke da ƙwayoyin a kowane lokaci.

"Su kan tafi dandalin sada zumunta su rika karo da abubuwa daban-daban. Ina fargabar bawa ƙananan yara na waya don tsoron abinda za su gani a dandalin sada zumunta. Abin ya lalace."

Alli-Macaulay ta ce rashin aikin yi ba dalili ne da zai sa matasa ɓarna ba, ta ƙara da cewa ba Najeriya kadai ne babu ayyukan yi ba.

DUBA WANNAN: 'Farautar 'yan bindiga suke yi' - Gwamnatin Kaduna ta yi karin haske kan jiragen sojoji da ke shawagi a jihar

"Na yi karatu a Burtaniya kuma na ga matasa da dama ba su da aikin yi amma ba su zama ɓata gari ba. Me zai sa ba zamu mu warware matsalolin mu da kanmu ba?" ta yi tambaya.

Ƴar majalisar ta ce dukkan wadanda suka yi karatun digiri na iya rungumar sana'ar hannu a maimakon kukan rashin aikin yi.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya ce maƙiyan Najeriya ne suka lalata zanga zangar EndSARs

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta ƙaryata iƙirarin da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya yi na cewa ita ce sanadin jinkirin rabon kayan tallafin korona a jihar.

Gwamnan yayin kare gwamnatinsa kan jinkirin rabon kayan tallafin ya ɗora kaifi kan Ministan Jinƙai da Kare Bala'i, Sadiya Umar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel