Hotuna: An kashe 'yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji - DHQ

Hotuna: An kashe 'yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji - DHQ

- Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram da suka yi yunkurin kai hari sansanin sojoji dake Damboa

- Rundunar sojojin ta Najeriya ta kwato makamai masu hadari da dama daga hannun maharan

- Sojojin Operation Lafiya Dole na cigaba da kai hari don korar ragowar mayakan Boko Haram da IS daga yankin

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe yan ta'adda 22 lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari sansanin sojoji da ke Damboa, Jihar Borno.

Jami'in yada Labaran hukumar sojin, Manjo Janar John Enenche, ya ce maharan sun sha luguden wuta daga jami'an sojoji.

A wani rahoto da aka fitar ranar Alhamis da aka yi wa take, "jami'an Operation Fire Ball" sun dakile harin mayakan Boko Haram,' lamarin ya faru ne a ranar 25 ga Oktoban 2020.

An kashe yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji
An kashe yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji. Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Farautar 'yan bindiga suke yi' - Gwamnatin Kaduna ta yi karin haske kan jiragen sojoji da ke shawagi a jihar

An ruwaito cewa an lalata tankar yaki guda biyu, sannan an kwaci bindigar baro jirgi kirar NSV, bindigar roket guda biyu, bindiga mai sarrafa kanta kirar PKT guda hudu, da wata irinta mai yin kowane aiki, da ma wasu da dama.

Sanarwar ta ce "sojojin Operation Fire Ball karkashin Operation Lafiya Dole suna ci gaba da kai hari kan mayakan Boko Haram da IS don karar da ragowar mayakan daga yankin."

An kashe yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji
An kashe yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji. @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kwamishina ya zubda hawaye bayan ganin 'satar' da 'yan daba suka yi a Kogi (Bidiyo)

A wani labarin, gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa makiyan kasar nan suka lalata zanga zangar #endsars da nufin rushe kasar.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata, 27 ga Oktoba a yayin tattaunawa da manema labarai kan yadda za a tabbatar da hadin kan Najeriya, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel