Gwanda lalatattun 'yan sanda da kwararrun 'yan ta'adda a Nigeria - Gwamna Abdulrazaq

Gwanda lalatattun 'yan sanda da kwararrun 'yan ta'adda a Nigeria - Gwamna Abdulrazaq

- Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya roki 'yan Nigeria da kada su taba juyawa 'yan sanda baya

- A cewarsa, gwanda lalataccen d'an sanda da kwararren dan ta'adda, kasancewar, ko da girgiza kurna ta fi magarya dadi

- Abdulrazaq ya ce zanga zangar #EndSARS da aka yi a makonnin baya, bai cancanci zama silar mayar da jami'an 'yan sanda saniyar ware ba

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya roki 'yan Nigeria da kada su taba juyawa 'yan sanda da sauran jami'an tsaro baya.

Ya ce, ko goma ta lalace tafi biyar al'barka, ma'ana, gwanda lalataccen d'an sanda da kwararren dan ta'adda.

Gwamna Abdulrazaq ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da ya karbi bakuncin sanatoci uku da ke wakiltar jihar a majalisar dattijai.

KARANTA WANNAN: Muna rokon a ba Kudu maso Gabas shugabancin kasa a zaben 2023 - Gwamna Umahi

Sanatocin sun ziyarci gwamnan ne domin jajanta masa, kan yadda wasu gurbatattun matasa suka fasa shaguna da dakunan ajiyar kayan abinci, suka sace na sacewa a jihar.

Ya ce da yawa daga cikin jami'an 'yan sandan sun kasance masu sadaukar da komai na su domin samun kyakkyawar Nigeria.

KARANTA WANNAN: Gwamnati ta lissafa muhimman wurare 22 da mabarnata suka lalata

Abdulrazaq ya ce abubuwan da suka faru a makonnin baya, musamman zanga zangar #EndSARS, bai cancanci zama silar mayar da jami'an 'yan sanda saniyar ware ba.

A cewar sa, cin fuska da mayar da 'yan sanda saniyar ware, zai iya zama wata baraka da za ta ba 'yan ta'adda damar aiwatar da munanan ayyukansu a cikin al'umma.

Gwanda lalatattun 'yan sanda da kwararrun 'yan ta'adda a Nigeria - Gwamna Abdulrazaq
Gwamna Abdulrazaq
Asali: UGC

A wani labarin, wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta hana takardar amincewa hukumar EFCC izinin cafke Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar albarkatun man fetur.

Ijeoma Ojukwu, mai shari'ar, ta ki amincewa da bukatar EFCC ne saboda gazawar hukumar na gabatarwa kotun shaidar kotu na kiranye ga ministar a baya.

Ta ce ya zama wajibi a gabatarwa kotu takardar shaidar goron gayyatar kotu ga tsohuwar ministar, kafin kotun ta amince ta bayar da izinin cafke Alison-Madueke.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel