Kwamishina ya zubda hawaye bayan ganin 'satar' da 'yan daba suka yi a Kogi (Bidiyo)

Kwamishina ya zubda hawaye bayan ganin 'satar' da 'yan daba suka yi a Kogi (Bidiyo)

- Lalata cibiyar lafiya ta miliyoyin Naira a kogi ya haifar da damuwa kwarai da gaske

- Kwamishinan lafiyar Kogi, Audu, ya fashe da kuka bayan ganin irin barnar da akayi wa kayayyakin aikin lafiyar

- Audu ya ce za a kashe makuden kuɗaɗe kafin sake dawo da wajen yadda yake

Kwamishinan lafiya a Jihar Kogi, Saka Audu, ya fashe da kuka ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba lokacin da yake duba irin barnar da masu fasawa da ƙona dukiyar al'umma suka yi a wata cibiyar lafiya a Jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Gidan talabijin na channels ya ruwaito cewa Audu ya bayyanawa manema labarai cewa kayayyakin miliyoyin naira masu barnar suka lalata.

Audu ya ce daga cikin abubuwan da aka lalata akwai na'urar 'Magnetic Resonance Imaging machine' (MRI) da 'Computer Mammography Machine' da kuma 'Digital Radiography.'

Kwamishina ya zubda hawaye bayan ganin satar da yan daba suka yi a Kogi
Kwamishina ya zubda hawaye bayan ganin satar da yan daba suka yi a Kogi. Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jinkirin rabon tallafin korona: FG ta mayar wa Gwamna Tambuwal martani

Yace:

"Kayayyakin biliyoyin naira duk an sace su. Wanda baza a iya dauka ba kamar su na'urar sanyaya dakin rugakafi, inda muke adana alluran rigakafi, an kuma lalata bangarorin (MRI) da (CT) yadda baza su gyaru ba.

"Wasu kayan kuma an dauke su daga ma'ajiya zuwa daji na kusa kuma an lalata su."

Kwamishinan lafiyar Jihar kogi ya kasa rike hawayensa akan irin barnar da akayi wa kayan aikin lafiyar.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Bartomeu ya yi murabus a matsayin shugaban Barcelona

A wani bidiyo da gidan talabijin na Channels ya wallafa an nuno kwamishinan yana goge hawaye da bayan hannun sa kuma ya na ƙokarin sa don dakatar da hawayen.

A wani labarin daban, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa makiyan kasar nan suka lalata zanga zangar #endsars da nufin rushe kasar.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata, 27 ga Oktoba a yayin tattaunawa da manema labarai kan yadda za a tabbatar da hadin kan Najeriya, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164