Rayyuka 21 sun salwanta yayin da trela ta yi karo da motar bas a Enugu

Rayyuka 21 sun salwanta yayin da trela ta yi karo da motar bas a Enugu

- Mummunan hatsari da ya faru a jihar Enugu ya yi sanadin rasuwar mutum 21 ciki har da yara 'yan makaranta

- Hukumar kiyayye haddura, FRSC, ta tabbatar da afkuwar hatsarin inda ta ce trela ce ta kubce ta fada wa motar daukan 'yan makarantar

- Kwamandan hukumar FRSC na jihar Ogbonna Kalu ya ce tukin ganganci da gudu fiye da ka'ida ne sanadin afkuwar hatsarin

Hukumar Kiyayye Haddura ta Kasa, FRSC, a ranar Alhamis ta tabbatar da rasuwar mutane 21 ciki har da yara 'yan makaranta sakamakon hatsarin mota a Mgbowo a karamar hukumar Awgu ta jihar Enugu.

Kwamandan rundunar ta Enugu, Mista Ogbonna Kalu wadda ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin a wayar tarho ya ce hatsarin ya faru ne a ranar Laraba da rana.

Da dumi-dumi: Rayyuka 21 sun salwanta yayin da trela ta yi karo da motar bas a Enugu
Taswirar Jihar Enugu: Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama ɗan ƙungiyar asirin da ake nema ruwa a jallo a wurin da akayi fashi da makami a Ogun

Ya ce trela ce da motar bas ta kai yara makaranta hatsarin ya ritsa da su.

Kwamandan ya ce gudu fiye da ka'ida ce dalilin afkuwar hatsarin da kuma tukin ganganci.

Kalu ya ce, "An tabbatar da mutuwar mutum 21 kuma fiye da mutane 50 ke cikin bas din.

"Kazalika, ba yara 'yan makaranta ne kadai suka mutu ba. Wadanda ke sana'a a gefen titi suma suna daga cikin wadanda suka rasu.

"Daga bayanin da muka samu, tukin ganganci ne ya janyo afkuwar hatsarin."

KU KARANTA: Jinkirin rabon tallafin korona: FG ta mayar wa Gwamna Tambuwal martani

Amma majiyar Legit.ng ta tattaro cewa abin bakin cikin ya faru ne a lokacin da trelar mallakar wani kamfanin gine-gine da ke aiki a Rafin Oji a Awgu ya kubce ya fada wa motar bus na 'yan makaranta dauke da yara fiye da 60 'yan Presentation Nursery and Primary School, Awgu.

A wani labarin daban, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa makiyan kasar nan suka lalata zanga zangar #endsars da nufin rushe kasar.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata, 27 ga Oktoba a yayin tattaunawa da manema labarai kan yadda za a tabbatar da hadin kan Najeriya, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel