'Yan bindiga sun yi awon gaba da farfesar Jami'ar Anambra

'Yan bindiga sun yi awon gaba da farfesar Jami'ar Anambra

- Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa ne sun sace wata farfesa da ke aiki a jami'a a Anambra

- Farfesar da ba a sanar da sunan ta ba tana hanyarta na komawa gida ne bayan halarton taron masu ruwa da tsaki sai suka tare ta

- Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta ce ta aike da jami'anta yankin da nufin ceto farfesan da kama wadanda suka sace ta

Wasu 'yan bindiga sun sace wata malamar jami'a mai mukamin farfesa wanda ba a bayyana sunanta ba ta Jami'ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, a jihar Anambra.

The Punch ta ruwaito cewa an sace malamar ne a hanyar Akwa daga jami'ar.

Shugaban kungiyar 'yan uwan juna ta Enugwu-Agidi, Ndubuisi Obijiofor ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da farfesar Jami'ar Anambra
'Yan bindiga sun yi awon gaba da farfesar Jami'ar Anambra. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Ya ce, "Muna sanar da jama'a sace wata mata da ya faru a hanyar Enugwu-Agidi zuwa Nawgu ranar Laraba da misalin 6:25 na yamma.

"Wadda aka sacen, farfesa ce a jami'ar Odumegwu Ojukwu da ke jihar Anambra, ta baro Akwa bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a makarantar, sai dai an sace ta kafin ta kai inda zata.

"Wannan shine karo na biyu da aka sace malaman jami'a a wajen da abin ya faru.

"Wajen da abin ya faru guri ne mai hadari, kuma masu bin hanyar suna da yiwuwar fadawa hannun bata gari.

DUBA WANNAN: An kama ɗan ƙungiyar asirin da ake nema ruwa a jallo a wurin da akayi fashi da makami a Ogun

"Shugabannin yankin Enugwu-Agidi suna sanar da al'umma cewa su guji bin wannan titin daga 6:30 na yamma saboda rashin tsaro, tare da shawartar mazauna yankin da su tabbatar da tsaro a yankin.

"Muna kuma kira ga gwamnatin jiha da ta tallafa mana wajen gyara titin don saukaka zirga zirga saboda tsaro. Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoton wadda aka sace tana hannun masu garkuwa da mutanen."

KU KARANTA: Jinkirin rabon tallafin korona: FG ta mayar wa Gwamna Tambuwal martani

Mai magana da yawon rundunar yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar al'amarin.

Ya ce, "duk da dai ba'a kawo rahoton a hukumance ba, Kwamishina John Abang, ya yi umarni da a binciki al'amarin, a ceto wadda aka sace, sannan a gano masu garkuwar don daukar mataki".

A wani labarin, Hukumar Kiyayye Haddura ta Kasa, FRSC, a ranar Alhamis ta tabbatar da rasuwar mutane 21 ciki har da yara 'yan makaranta sakamakon hatsarin mota a Mgbowo a karamar hukumar Awgu ta jihar Enugu.

Kwamandan rundunar ta Enugu, Mista Ogbonna Kalu wadda ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin a wayar tarho ya ce hatsarin ya faru ne a ranar Laraba da rana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel