Gidan yari ta ƙi ƙarbar ɓata gari da ƴan daba da ƴan sanda suka gurfanar

Gidan yari ta ƙi ƙarbar ɓata gari da ƴan daba da ƴan sanda suka gurfanar

- An fara gurfanar da mutanen da aka kama kan zargin barnata kayayyaki da wasu laifuka yayin zanga-zangar EndSARs a Legas

- An dawo da kimanin mutane 200 zuwa ofishin ƴan sanda bayan gurfanar da su a kotu

- Hakan ya faru ne domin gidajen gyaran halin ba za su karɓe su ba har sai an musu gwajin cutar Korona an tabbatar ba su ɗauke da cutar

Gwamnatin jihar Legas ta fara gurfanar da dukkan wadanda ake zargin ƴan daba ne da suka yi ɓarna a jihar bayan harbe-harben Lekki tollgate.

A ƙalla mutane 520 da ake zargi ne ƴan sanda suka kama da ake zargi da ƙone-ƙone, kisa, sata da wasu laifukan.

Kakakin ƴan sandan jihar, Muyiwa Adejobi ya shaidawa The Punch a ranar Laraba cewa an gurfanar da fiye da mutum 200 cikin 520 da aka kama.

Gidan yari ta ƙi ƙarbar ɓata gari da ƴan daba da ƴan sanda suka gurfanar
Gidan yari ta ƙi ƙarbar ɓata gari da ƴan daba da ƴan sanda suka gurfanar. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama ɗan ƙungiyar asirin da ake nema ruwa a jallo a wurin da akayi fashi da makami a Ogun

Sai dai wakilin majiyar Legit.ng ya gano cewa an dawo da wadanda ake zargin ofishin ƴan sanda bayan kai su kotu a maimakon basu masauki a gidan yari.

An gano cewa hukumar kula da gidajen gyaran hali da ƙi ƙarbar wadanda ake zargin ƴan daban ne don rashin wurin da za a ajiye su duba da cewa akwai barazanar COVID 19.

Adejobi ya ce, "Mun fara gurfanar da mutum 520 da muke zargin ƴan daba ne. Muna ta raba su zuwa ofishin daban-daban don Shari'a ta jiha ce don haka muna da ikon ajiye su a ofishin mu."

Adejobi ya ce ba wadanda ake zargi da ɓarnar bane kawai gidan yarin ta ƙi karba.

KU KARANTA: Jinkirin rabon tallafin korona: FG ta mayar wa Gwamna Tambuwal martani

Ya ce, "A yanzu duk lokacin da muka gurfanar da wadanda ake zargi a kotu, mu kan dawo da su ofishin mu saboda korona. Daga nan sai muyi musu gwajin COVID 19 kafin a karɓe su a gidan gyaran hali."

Kakakin hukumar kula da gidajen gyaran hali na Legas, Rotimi Oladokun ya ce "bashi da masaniya kan labaran rashin karbar ƴan daban amma ya ce doka ce yanzu sai an yi gwajin korona kafin a kai mutum gidan. Wadanda suke da cutar gwamnati za ta kai su wurin magani sai sun warke sai a dawo da su."

"Maganar ƙin karba bai taso ba. Wannan ba gaskiya bane."

A wani labarin, gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa makiyan kasar nan suka lalata zanga zangar #Endsars da nufin rushe kasar.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata, 27 ga Oktoba a yayin tattaunawa da manema labarai kan yadda za a tabbatar da hadin kan Najeriya, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel