Ba yunwa ta sa ake satan kayan tallafin Korona ba, kwadayi ne kawai - Fadar shugaban kasa

Ba yunwa ta sa ake satan kayan tallafin Korona ba, kwadayi ne kawai - Fadar shugaban kasa

- Yayinda ake fara bi gida-gida ana kwace kayayyakin da mutane suka wawara, fadar shugaban kasa ta yi tsokaci

- Femi Adesina ya ce shi a tunaninsa wadanda suka debi kayan tallafi Koronan da gwamnoni suka ki rabawa barayi ne

- Femi ne babban mai bawa shugaba Buhari shawara kan kafafen yada labarai

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa ba talauci ta tunzura mutane wawushe runbunan abinci da shaguna ba a fadin tarayya, kwadayi ce kawai.

Adesina wanda ya bayyana hakan a hirar da yayi a shirin Sunrise Daily na tashar Channels TV ya ce malalata da batagari ne kawai sukayi amfani da zanga-zanga wajen satan kayan abinci.

Ya ce sam bai amince da bayanan da wasu ke yi ba cewa yunwa ta sa mutane ke wawusan kayan abinci ba.

"Ban yarda da maganar nan (cewa masu wawusa yunwa suke ji ba) saboda laifi laifi ne, ta yaya zata halatta sata saboda kawai mutum na jin yunwa, "yace.

"Kamar yadda ba zaka halatta fashi da makami don mutum na fama da talauci ba, ba zaka iya halatta sace-sacen da ake yi yanzu ba. Wannan barandanci ne zalla."

"Ba dukkan wadanda ke wawusan ke jin yunwa ba, maganar gaskiya kenan. Zallan kwadayi ne kawai da laifi," Adesina ya kara.

Ya kara da cewa halin da kasar ke ciki ta haifar da rikici a ko ina kuma ta bada daman sace-sace da fashe-fashe.

KU KARANTA: Bayan watanni 6 da saukeshi, Ganduje ya dawo da Muazu Magaji cikin gwamnatinsa

Ba yunwa ta sa ake satan kayan tallafin Korona ba, kwadayi ne kawai - Fadar shugaban kasa
Ba yunwa ta sa ake satan kayan tallafin Korona ba, kwadayi ne kawai - Fadar shugaban kasa Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

A bangare guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba ma matasan Borno, kan kin shiga sahun masu barnar kaya da sace-sace sakamakon zanga-zangar EndSARS da aka yi a kasar.

Karamin ministan noma, Alhaji Buba Shehuri ne ya bayyana hakan, inda ya ce Buhari ya jinjinawa matasan a wani sakon fatan alkhairi zuwa ga kungiyar masu ruwa da tsaki na zaman lafiya a ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, a Maiduguri.

A cewarsa, Buhari na matukar alfahari da matasan Borno wadanda suka nuna halin dattako da nagarta ta hanyar kin shiga rikicin karkashin fakewa da zanga-zangar EndSARS.

KU KARANTA: Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure

Don samun manhajar Legit Hausa, latsa kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel