Bayan makonni biyu, Ganduje ya mayar da Dawisu bakin aikinsa

Bayan makonni biyu, Ganduje ya mayar da Dawisu bakin aikinsa

- Daga karshe, Ganduje ya mayar da Dawisu bakin aikinsa bayan makonni biyu

- Hadimin Buhari Bashir Ahmad ya ce ba shi da hannu a dakatad da Dawisu

- Dawisu ya mika godiyarsa ga abokan arziki da suka taya shi da addu'a

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo da Salihu Tanko Yakassai, wanda aka fi sani da Dawisu, bakin aikinsa na babban hadiminsa na kafafen yada labarai.

Ganduje ya yi hakan ne makonni biyu bayan dakatad da shi daga mukaminsa kan sukan shugaba Muhammadu Buhari da yayi a shafinsa na Tuwita.

Salihu Tanko Yakassai ya bayyana hakan da safiyar Juma'a a shafinsa na Tuwita inda ya mika godiyarsa ga jama'an da suka taya sa farin cikin komawa bakin aiki.

Yace: "Ina mika godiya ga dukkan wadanda suka kira ne ko suka tura sakonnin taya murnan mayar da ni mai bada shawara kan kafafen yada labarai ga gwamnan Umar Ganduje, bayan makonni biyu da dakatad da ni."

"Ina godiya gareku bisa goyon bayanku da addu'o'inku."

KU DUBA: ASUU: Muddin za a cigaba da rike mana albashi, yajin-aiki ba zai kare ba

KU KARANTA: WTO: Myung-hee ta san aiki, shiyasa mu ke mara mata baya inji Amurka

A ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba, 2020, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da hadiminsa, Salihu Tanko Yakasai daga aiki.

Tanko ya wallafa a Twitter cewa, "ban taba ganin gwamnati da bata da tausayi ba kamar ta shugaban kasa Buhari. Sau da yawan lokuta idan jama'arsa suna fuskantar matsala, a maimakon ya tausasa musu tunda shine bangonsu, sai ya kasa hakan.

"Yadda yake nuna bai damu da al'amuran jama'a ba yayi yawa,"

"Yi wa jama'arka jawabi a kan abinda ke matukar damunsu ya zama tamkar wata alfarma da za ka yi musu."

Bayan makonni biyu, Ganduje ya mayar da Dawisu bakin aikinsa
Bayan makonni biyu, Ganduje ya mayar da Dawisu bakin aikinsa Hoto: @Dawisu
Asali: Twitter

Wasu sun fito su na zargin wani hadimin shugaba Muhammadu Buhari da hannu a wannan dakatarwar da aka yi wa mai ba gwamnan na Kano shawara.

Hadimin shugaban kasar da ake tuhuma da wannan aiki shi ne Malam Bashir Ahmaad.

Kamar Salihu Yakasai, Malam Bashir Ahmaad ya fito ne daga jihar Kano, kuma ana tunanin ya na da alaka mai kyau da gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel