Zanga zangar EndSARS: 'Yan sandan Kaduna sun kama mutum 23, sun kwato babura 14

Zanga zangar EndSARS: 'Yan sandan Kaduna sun kama mutum 23, sun kwato babura 14

- Rundunar ƴan sandan ta ce za ta ci gaba da da bincike har sai sun tabbatar da dawowar zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa

- An gano babura 14 da adaidaita sahu guda 6 daga cikin kayan da aka sace da sunan tallafin korona

- Tuni dai har an tura wasu daga cikin mutanen da ake zargi da satar kayan tallafin kotu don ayi musu shari'a

Rundunar ƴan sanda ta jihar Kaduna cafke mutane 23 da ake zargi da satar kayan tallafin korona kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Rundunar ƴan sanda ta jihar Kaduna ta kama mutane 23 da ake zargi da fasa ɗakin adana kayayyaki lokacin zanga zangar EndSARS, ta kuma gano babura guda 14 da babur mai kafa uku (adaidata).

DUBA WANNAN: WASSCE 2020: WAEC ta sanar da sabon ranar da za ta fitar da sakamakon jarrabawa

Zanga zangar EndSARS: 'Yan sandan Kaduna sun kama mutum 23, sun kwato babura 14
Zanga zangar EndSARS: 'Yan sandan Kaduna sun kama mutum 23, sun kwato babura 14. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Muhammad Jalige ne ya bayyana haka, a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kaduna ranar Laraba.

Jalige ya ce an kama wanda ake zargin ranar Talata a yankunan Barnawa, Narayi da Kakuri a kananan hukomomin Chikun da Kaduna South.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya ce maƙiyan Najeriya ne suka lalata zanga zangar EndSARs

Ya ce zasu tura wanda wanda ake zargi kotu, ya kuma ce zasu cigaba da bincike har sai sun tabbatar da zaman lafiya ya dawo a yankunan da abin ya shafa a jihar.

Tuni aka dai aka tura wasu mutane 25 da ake zargi ranar Litinin.

A wani labarin daban, wani ɗan kasuwa mazaunin Legas mai suna Afeez Mojeed ya bayyana cewa mataimakin kwamishinan ƴan sanda, DCP, Abba Kyari ya tatsi naira miliyan 41 daga hannunsa.

Mojeed ya yi iƙirarin cewa wannan lamarin ya faru ne a shekarar 2014 lokacin Kyari shugaban tsohuwar rundunar SARS a Legas kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel