Ku kwantar da hankulanku, ba za'a yi wahalan mai a Kano da wasu jihohin Arewa ba - IPMAN

Ku kwantar da hankulanku, ba za'a yi wahalan mai a Kano da wasu jihohin Arewa ba - IPMAN

- Mazauna birnin tarayya sun waye gari babu man fetur a gidajen mai

- Wakilin Legit ya gano cewa tun ranar Asabar aka fara rashin mai a Abuja

- Idan aka kara yan kwanaki a haka sauran jihohin Najeriya zasu fara fuskantar haka

Kungiyar yan kasuwa mai masu zaman kansu IPMAN, shiyar jihar Kano ta kwantar da hankalin mutane kan rahotannin cewa za'ayi wahalan mai sakamakon zanga-zangan #EndSARS.

IPMAN ta bayyana hakan ne ranar Laraba a Kano.

Shugaban kungiyar, Bashir Dan-Malam ya bada wannan tabbaci ne bayan ziyarar aiki da yayi na daukan man fetur bayan tsaikon da aka samu sakamakon zanga-zangar #EndSARS.

A cewarsa, "Babu bukatar masu motoci da jama'an gari su tayar da hankali ta hanyar sayan mai fiye da wanda ake bukata saboda kungiyar na kokarinta wajen kai mai dukkan jihohin dake karkashin Kano, Katsina, Bauchi, Yobe da Jigawa.

"Za mu cigaba da goyon bayan gwamnatin tarayya wajen tabbatar da isasshen mai dukkan sassan kasar nan,"

KU KARANTA: Don hana dalibai masu Hijabi shiga makaranta, an bankawa ofishin shugaban makaranta wuta

Ku kwantar da hankulanku, ba za'a yi wahalan mai a Kano da wasu jihohin Arewa ba - IPMAN
Ku kwantar da hankulanku, ba za'a yi wahalan mai a Kano da wasu jihohin Arewa ba - IPMAN Credit: @NNPCgroup
Asali: Twitter

KU DUBA: Saura mataki guda, Ngozi Okonjo-Iweala ta zama sabuwar shugabar kungiyar kasuwancin duniya WTO

Legit ta ruwaito muku cewa ana fuskantar matsalar rashin man fetur a Birnin Abuja da ma kewayenta yayinda gidajen mai suke cike makil da dogon layi na ababen hawa a babban birnin tarayyar ranar Talata.

kamfanin man fetur na kasa, NNPC ta zargi zanga-zangar ENDSARS akan matsalar, amma tana fatan daga baya dogon layin man zai sassauta daga baya ranar Talatar.

Mai magana da yawun kamfanin, Dr Kennie Obateru yace da yawa daga cikin yan kasuwa suna samun man kuma za;a samu daidaito a matsalar man nan ba da dadewa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel