Don hana dalibai masu Hijabi shiga makaranta, an bankawa ofishin shugaban makaranta wuta

Don hana dalibai masu Hijabi shiga makaranta, an bankawa ofishin shugaban makaranta wuta

- Har yanzu, dalibai basu daina fuskantar tsangwama kan irin tufafin da suke sanyawa ba

- Yayinda ake hana wasu shiga don sun sanya Hijabi, ana hana wasu shiga don bayyana tsiraici

An samu tashin hankali a garin Machinga dake kasar Malawi inda wasu matasa suka bankawa ofishin shugaban makarantar firamare wuta.

Matasan sun aikata hakan ne don shugaban makarantan ya hana dalibai masu Hijabi shiga aji, BBC Hausa ta ruwaito.

Wannan abu ya faru ne a makarantan firamaren Mpiri mallakar cocin Katolika.

Jami'an yan sandan yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin kuma sun ce an kone ofishin kurmus.

Garin Machinga na da mazauna masu mabanbantan addini musamman Musulmai da Kirista, amma mafi akasarin makarantun garin mallakin Kiristoci ne.

An ruwaito cewa babu wata dokar gwamnati da ta ayyana irin kayan da ɗalibai za su saka, sai dai makarantun kan hana ɗalibai saka hijabi, abin da ke jawo rikici daban-daban.

Makarantun sun yi barazanar rufewa saboda tashin hankalin da ke faruwa a yanzu.

DUBA NAN: Hankula sun tashi a Ibadan saboda hana dalibai mata sanya Hijabi a makarantar sakandari

Don hana dalibai masu Hijabi shiga makaranta, an bankawa ofishin shugaban makaranta wuta
Don hana dalibai masu Hijabi shiga makaranta, an bankawa ofishin shugaban makaranta wuta
Asali: Depositphotos

DUBA NAN: Gwamnati ta dura kan ASUU game da amfani da UTAS wajen biyan albashi

A wani labarin mai alaka, kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeriya MURIC, ta bayyana rashin jin dadinta kan korar daliba daga makarantar sakadandaren jami'ar Ibadan, Ikhlas Badiru, daga makaranta.

Shugabar makarantar da kanta mai suna, Phebean Olowe, ta sallami dalibar.

Diraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, a wani jawabi da ya saki ranar Litinin ya nuna bacin ransa kan wannan abu.

Yace: "Ya bayyana karara cewa shugabar makarantar bata iya sulhu ba kuma bata ki abubuwa su tabarbare ba."

"A Turai da Amurka inda Musulmai ba su yawa, an halatta sanya hijabi a makarantu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel