An kama ɗan ƙungiyar asirin da ake nema ruwa a jallo a wurin da akayi fashi da makami a Ogun

An kama ɗan ƙungiyar asirin da ake nema ruwa a jallo a wurin da akayi fashi da makami a Ogun

- Rundunar yan sanda ta cafke wani dan kungiyar asiri da ta daɗe tana nema

- Rundunar tace sunansa ya dade a takardar mutanen da ake nema ruwa a jallo

- An kama wanda ake zargin a wajen da aka aikata laifin fashi da makami

Rundunar ƴan sanda ta jihar Ogun ta ce ta samu nasarar kama shahararren ɗan kungiyar asirin nan da ake nema ruwa a jallo, Akibu Tikare, a wurin da akayi fashi da makami a Ogijo, karamar hukumar Sagamu, Jihar Ogun.

Tikare, wanda ake zaton shine shugaban k'ungiyar asirin Eiye Confraternity, an kama shi ne a wani harin fashi da makami a tsakanin Gbaja da Kamalo a Ogijo.

An kama ɗan ƙungiyar asirin da ake nema ruwa a jallo a wurin da akayi fashi da makami
Kwamishinan 'yan sandan Ogun, Edward Ajogun. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: EndSARS: Legos ta sake rikicewa yayin da yan tawaye suka lalata motocin BRT, suka fasa shaguna

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sanda, DSP Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya fitar ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Oyeyemi ya ce ƴan sandan Ogijo ne suka samu nasarar kama shi ranar Asabar lokacin da yake tsaka da kwacewa mutane dukiyar su.

A jawabin da rundunar ta wallafa, Gagarumin shugaban kungiyar asiri ta Eiye, wanda ke jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo na rundunar yan sanda, ya fada komar jami'an yan sandan shiyyar Ogijidi ranar Asabar, 24 ga Oktoba a wurin da akayi fashin.

KU KARANTA: Mutum 13 ne suka rasu a hadarin mota a babban titin Kano zuwa Kaduna

"Wanda ake zargin, Akibu Tikare mai shekaru 26, an kama shi sakamakon wani kiran gaggawa da akayi wa Ofishin Ogijo da misalin 9:30 na dare cewa wasu gun-gun yan daba suna zirga zirga a yankin Gbaga da Kamalu na Ogijo suna yi wa mutane fashin kayayyaki.

"Da yake karbar rahoto, DPO na ofishin Ogijo, CSP Muhammad Suleiman Baba, ya yi gaggawar tura jami'an ƴan sanda yankin da wasu jami'an sintiri, inda suka kama wanda ake zargin, wasu kuma da ake zargin sun fito daga yankin Ikorodu da Owutu na Lagos, sun gudu."

A wani labarin, Kwamishinan ƴan sandan Legas, Hakeem Odumosu, a ranar Talata, ya ce sun kama mutum 520 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da ƙone-ƙone, fashi, kisan da kuma mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya lokacin zanga zangar Endsars.

Mr Odumosu ya shaidawa yan jarida a hedikwatar Ikeja, cewa an kama masu laifin ne a laifukan da aka aikata sakamakon karya doka lokacin zanga zangar EndSARS a cewar rahoton Premium Times.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel