Gwamna Ganduje ya ce maƙiyan Najeriya ne suka lalata zanga zangar EndSARs

Gwamna Ganduje ya ce maƙiyan Najeriya ne suka lalata zanga zangar EndSARs

- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi ikirarin cewa wasu mutane wanda basa son ganin ci gaban Najeriya ne suka bata zanga zangar #EndSars

- Ganduje ya bayyana cewa ainihin zanga zangar da aka fara don nuna rashin amincewa da zaluncin ƴan sanda tana da dalili mai karfi

- Gwamnan ya ce maƙiyan Najeriya ne suka haddasa fitina a cikin zanga zangar saboda bukatar su

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa makiyan Kasar nan suka lalata zanga zangar #endsars da nufin rushe kasar.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata, 27 ga Oktoba a yayin tattaunawa da manema labarai kan yadda za a tabbatar da hadin kan Najeriya, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Gwamna Ganduje ya ce maƙiyan Najeriya ne suka lalata zanga zangar EndSARs
Abdullahi Ganduje. @RanoMurtala / Twitter
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutum 5 sun mutu yayin rabon kuɗin da suka tsinnta a ma'ajiyar kayan tallafin korona

Ya bayyana cewa da yawa daga cikin manyan jami'ai suna goyon bayan zanga zangar lumana ta #Endsars da aka fara don nuna kyamatar zaluncin ƴan sanda.

Sai dai, Gwamnan ya yi iƙirarin cewa maƙiyan Najeriya ne suka yi amfani da yanayin wajen ganin sun rusa kasar.

A cewar Ganduje:

"Asalin zanga zangar ana magana ne akan zaluncin jami'an SARS da kashe mutane ba bisa ka'ida ba, wanda babbar matsala ce kuma da yawan mu mun goyi bayan zanga zangar, tare da yin kira da ayi wa hukumar ƴan sanda kwaskwarima.

KU KARANTA: EndSARS: Legos ta sake rikicewa yayin da yan tawaye suka lalata motocin BRT, suka fasa shaguna

Amma abun da ke faruwa yanzu ya tabbatar da cewa; maƙiyan Najeriya ne suka zauna suka kuma yi shawarar bari su rusa ƙasar. Amma Allah yana tare damu; basu yi nasara ba."

Ya kuma bayyana cewa duka mai addu'ar ganin bayan Najeriya cikakken mahaukaci ne, ya kuma yi kira da hadin kan ƙasa, musamman daga matasa.

A wani labarin, Sanatocin yankin kudu maso yamma sun kaiwa gwamnan Lagos, Babajide sanwo-Olu, don jajanta masa akan barnar da akayi satin daya gabata akan kayayyakin gwamnati dana daidaikun mutane a jahar.

Sanatocin kudu maso yamma karkashin jagorancin Sanata Ajayi Boroffice (Ondo North) sun kai wa gwamnan ziyarar ne a gidansa dake Marina ranar Talata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel