Jinkirin rabon tallafin korona: FG ta mayar wa Gwamna Tambuwal martani

Jinkirin rabon tallafin korona: FG ta mayar wa Gwamna Tambuwal martani

- Gwamnatin tarayya ta mayarwa gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal martani kan jinkirin rabon tallafin korona

- Gwamnatin tarayyar ta ƙaryata iƙirarin da Tambuwal ya yi na cewa bata raba kayan a kan lokaci ba

- Gwamnatin ta kuma ce ba gaskiya bane cewa ta bada umurnin a jinkirta sai kayan sun taru inda ta ce ba ta da ikon fadawa jihohi yadda za su mulki jiharsu

Gwamnatin tarayya ta ƙaryata iƙirarin da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya yi na cewa ita ce sanadin jinkirin rabon kayan tallafin korona a jihar.

Gwamnan yayin kare gwamnatinsa kan jinkirin rabon kayan tallafin ya ɗora kaifi kan Ministan Jinƙai da Kare Bala'i, Sadiya Umar.

Jinkirin rabon tallafin korona: FG ta mayar wa Gwamna Tambuwal martani
Aminu Tambuwal. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Mutum 5 sun mutu yayin rabon kuɗin da suka tsinnta a ma'ajiyar kayan tallafin korona

Ya ce ministar ce ta bada umurnin a jira sai kayan tallafin sun taru gaba ɗaya sannan ta nemi a jira sai ta zo sannan a fara rabon.

A martanin da gwamnatin ta yi, ta ce bata son yin musayar kalamai da gwamnan jihar Sokoton.

Amma, ta ce gwamnan ba gaskiya ya fadi ba, don ba ta da iko kan yadda gwamnoni za su mulki jiharsu.

Da ya ke martani kan iƙirarin gwamnan a hirar tarho da Vanguard, majiya daga Ma'aikatar Jinƙai da Cigaba Al'umma da Kare Bala'i, ya bukaci gwamnan ya amsa laifinsa na jinkirin raba wa al'ummar jiharsa kayan.

KU KARANTA: EndSARS: Legos ta sake rikicewa yayin da yan tawaye suka lalata motocin BRT, suka fasa shaguna

Majiyar, wadda ya ƙaryata iƙirarin gwamnan na cewa makonni biyu da suka gabata aka aike wa jiharsa kayan abincin, ya yi bayanin cewa an raba kayan tun farkon lokacin da annobar ta ɓarke ƙasar, inda ya ce wadanda suka gaza yin aikinsu su dena ɗora wa gwamnati laifi.

A cewar majiyar, Ma'aikatar da gwamnatin tarayya ba su da ikon fada wa jihohi yadda za su gudanar da harkokinsu.

"Abinda muka sani a matsayin mu na ma'aikata, munyi iya ƙoƙarin mu na ganin mun raba kayan tallafin ga jihohi a kan lokaci don su raba wa al'ummarsu.

"Idan wasu dalilai sun saka jihohin sunyi jinkirin rabon kayan, ba laifin ma'aikatar bane," ya ƙara da cewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel