An garkame Sojojin da aka kama suna zabgan matasan da suka saba dokar hana fita

An garkame Sojojin da aka kama suna zabgan matasan da suka saba dokar hana fita

- Hukumar Sojin saman Najeriya ta yi tsokaci kan zargin cin zarafi da take hakkin dan Adam da aka yiwa wasu jami'anta

- Hukumar ta yi Alla-wadai da abinda Sojojin suka yi

- A cewar hukumar, abinda jami'anta sukayi ya sabawa ka'idojin da koyarwanta

Hukumar Mayakan saman Najeriya ta damke wasu jami'anta da aka gani a faifan bidiyo suna zabgan wasu matasa da suka saba dokar hana fita a jihar Osun.

A wani jawabi ranar Laraba, 28 ga Oktoba, ta shafinta na Tuwita, hukumar tace an damke hafsoshin ne bayan bidiyo ya nunasu karara suna zane mutane a garin Ilesha.

Hukumar ta ce ba zata lamunci irin wannan abu ba saboda ba ta yarda da take hakkin dan adam ba.

Air Force ta ce dukkan abinda Sojojin sukayi ya sabawa koyarwanta.

KU KARANTA: Don hana dalibai masu Hijabi shiga makaranta, an bankawa ofishin shugaban makaranta wuta

An garkame Sojojin da aka kama suna zabgan matasan da suka saba dokar hana fita
An garkame Sojojin da aka kama suna zabgan matasan da suka saba dokar hana fita Credit: @NIgAirForce
Asali: Twitter

KARANTA WANNAN: Saura mataki guda, Ngozi Okonjo-Iweala ta zama sabuwar shugabar kungiyar kasuwancin duniya WTO

Kalli bidiyon:

A wani labarin daban, 'yan kungiyar Boko Haram 22 ne suka mutu, yayin da sojoji 5 suka rasa rayukansu sakamakon wani gumurzu daya turnike tsakanin Sojoji da 'yan ta'addan.

Wata majiya tace 'yan Boko Haram din sun kai wa sojojin da ke Damboa hari a ranar Litinin. Sojojin sun ragargajesu na tsawon awanni 5.

Sakamakon haka ne sojoji 5 suka rasa rayukansu, 2 kuma suka samu raunuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel