Legas ba za ta iya daukan nauyin asarar da aka yi mata ba - Sanataocin jihohin Yarabawa

Legas ba za ta iya daukan nauyin asarar da aka yi mata ba - Sanataocin jihohin Yarabawa

- Sanata Boroffice ya jagoranci tawagar sanatocin kudu maso yamma don jajantawa gwamna Sanwa- Olu

- Boroffice ya ce zasu hada kai da gwamnatin tarayya don gyara inda aka lalata

- Sanwa-Olu yace zasu mika alhakin bincike ga hukumar data dace kan harin Lekki don daukar mataki

Sanatocin yankin kudu maso yamma sun kaiwa gwamnan Lagos, Babajide sanwo-Olu, don jajanta masa akan barnar da akayi satin daya gabata akan kayayyakin gwamnati dana daidaikun mutane a jahar.

Sanatocin kudu maso yamma karkashin jagorancin Sanata Ajayi Boroffice (Ondo North) sun kai wa gwamnan ziyarar ne a gidansa dake Marina ranar Talata kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Legas ba za ta iya daukan nauyin asarar da aka yi mata ba - Sanataocin jihohin Yarabawa
Legas ba za ta iya daukan nauyin asarar da aka yi mata ba - Sanataocin jihohin Yarabawa. Hoto daga @channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: EndSARS: Legos ta sake rikicewa yayin da yan tawaye suka lalata motocin BRT, suka fasa shaguna

A wata sanarwa da sakataren yada Labaran gwamnan, Gboyeka Akosile ya fitar, yace sai da Sanatocin suka gaji da ganin hotunan gine ginen da aka lalata a Lagos.

Da yake maida martani, Sanata Boroffice ya bayyana barnar a matsayin "rikitattaccen al'amari" kuma dole sai an tsananta binkice.

Ya bayyana damuwarsa kan matasan da aka lalatawa guraren sana'a, inda yace hakan na iya maida su yan zaman kashe wando.

"Munzo nan ne don jajanta maka akan abubuwa marasa dadi da suka faru a Lagos. Gwamnati da daidaikun mutane sun tafka mummunar asara a lalace lalacen da suka faru a zanga zangar #endsars," kamar yadda ya bayyana.

KU KARANTA: Mutum 5 sun mutu yayin rabon kuɗin da suka tsinnta a ma'ajiyar kayan tallafin korona

Ya kuma bayyana cewa gwamnati tayi duk mai yiwuwa don biya ma masu zanga zangar bukatar su. Sai dai wasu suna bukatar sai anyi wa kundin tsarin mulki gyara kuma hakan bazai yiwu nan take ba.

"A shirye muke da yin gyara."

Sanatocin hadi da gwamnatin tarayya a shirye suke don gyara guraren da suka lalace.

Sanata Boroffice yace zasu mika kuduri gaban majalisa don duba yiwuwar turawa yan Najeriya da suke waje suga irin barnar da aka aikata.

A nasa jawabin sanwo-Olu yayi godiya ga Sanatocin tare da kira da a zauna lafiya.

Ya kuma yi Allah wadai da harbin da akayi wa masu zanga zanga a Lekki da sojoji suka yi, inda yace bincike ne kadai zai tabbatar da adadin rayukan da aka rasa.

Ya kuma yi alkawarin cewa zasu mika alhakin binciken ga Hukumar data dace don daukar mataki.

A wani labarin daban, Kwamishinan ƴan sandan Legas, Hakeem Odumosu, a ranar Talata, ya ce sun kama mutum 520 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da ƙone-ƙone, fashi, kisan da kuma mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya lokacin zanga zangar Endsars.

Mr Odumosu ya shaidawa yan jarida a hedikwatar Ikeja, cewa an kama masu laifin ne a laifukan da aka aikata sakamakon karya doka lokacin zanga zangar EndSARS a cewar rahoton Premium Times.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel