Zulum zai dauki nauyin karatun yaran CJTF da Boko Haram ta kashe tun 2013

Zulum zai dauki nauyin karatun yaran CJTF da Boko Haram ta kashe tun 2013

- Ya yi alkawarin N180m, buhuhunan hatsi da kwalayen abinci 27,000 ga mayaka 9000

- Gwamnan ya shirya tsarin taimakawa matasan jami'an sa kai da aka kashe

- Ya mika godiyar al'ummar Borno ga iyalan yan sa kai bisa sadaukarwan da sukayi

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince daukan lauyin karatun yara marayu, wadanda iyayensu suka kasance yan Civilian JTF, mafarauta da yan banga da suka rasa rayukansu a filin daga Boko Haram a shekaru bakwai da suka gabata.

Zulum ya kaddamar da asusun lamunin N50,000 ga ko wacce cikin matan wadanda suka rasa rayukansu a yakin Boko Haram sannan kuma a rabawa yan CJTF masu yakan Boko Haram 9000 dake fafatawa yanzu kudi N180m, buhuhuban hatsin da kwalayen abinci 27,000.

Gwamnan ya sanar da dukkan wadannan tallafin a ranar Laraba a Maiduguri, yayinda yake jawwabi ga yan sa kai 9,000 da ke yakan Boko Haram tare da Sojoji a Borno.

An tara yan sa kan ne a cikin jami'ar jihar Borno.

Kowanne daga cikin yan sa kai zai samu kudi N20,000, buhun shinkafa kilo 50, kwalin taliya daya da galan mai daya, kuma dukkan hakan bai cikin albashinsu na wata.

KU KARANTA: Bayan rikice-rikice da zanga-zanga, Birtaniya ta bude ofishin jakadancinta dake Najeriya

Zulum zai dauki nauyin karatun yaran CJTF da Boko Haram ta kashe tun 2013
Zulum zai dauki nauyin karatun yaran CJTF da Boko Haram ta kashe tun 2013 Credit: @GovBorno
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hukumar NSCDC ta sallami hafsan da aka gani a bidiyo yana wawason kayan abinci a Abuja (Bidiyon)

Zulum zai dauki nauyin karatun yaran CJTF da Boko Haram ta kashe tun 2013
Zulum zai dauki nauyin karatun yaran CJTF da Boko Haram ta kashe tun 2013 Credit: @GovBorno
Asali: Twitter

Zulum zai dauki nauyin karatun yaran CJTF da Boko Haram ta kashe tun 2013
Zulum zai dauki nauyin karatun yaran CJTF da Boko Haram ta kashe tun 2013 Credit: GovBorno
Asali: Twitter

A bangare guda, 'yan kungiyar Boko Haram 22 ne suka mutu, yayin da sojoji 5 suka rasa rayukansu sakamakon wani gumurzu daya turnike tsakanin Sojoji da 'yan ta'addan.

Wata majiya tace 'yan Boko Haram din sun kai wa sojojin da ke Damboa hari a ranar Litinin. Sojojin sun ragargajesu na tsawon awanni 5.

Sakamakon haka ne sojoji 5 suka rasa rayukansu, 2 kuma suka samu raunuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel