Bayan rikice-rikice da zanga-zanga, Birtaniya ta bude ofishin jakadancinta dake Najeriya

Bayan rikice-rikice da zanga-zanga, Birtaniya ta bude ofishin jakadancinta dake Najeriya

- Bayan kusan mako daya da rufe ofishin jakadancinta, an bude ranar Talata

- An rufe cibiyoyin neman bizan ne sakamakon kone-kone da ake yi jihar Legas

- Dubunnan yan Najeriya na zuwa kasar Birtaniyya domin karatu da aiki

Ofishin jakadancin kasar Birtaniya ta sanar da bude cibiyoyin neman biza dake Najeriya.

An kulle ofishohin jakadancin ne ranar Alhamis da ya gabata sakamakon rikice-rikicen da suka biyo bayan zanga-zangar #EndSARS a fadin kasar.

A jawabin da ta saki a Tuwita, hukumar ya ce cibiyoyinta na aiki tukuru wajen biyawa mutanen suka nemi biza bukatunsu.

Amma za'a sake kulle cibiyoyin ranar Alhamis, saboda hutun murnar bikin Maulidi da gwamnatin tarayya ta bayar.

"Cibiyoyin neman bizanmu a Najeriya sun koma aiki yanzu. Sakamakon rufewan da mukayi, mun kokarin tukuru wajen baiwa masu neman biza da suka bukata tun a baya," yace.

"Mun gode bisa hakurinsu da fahimta. Ku sani cewa zamu sake rufewa ranar 29 ga Oktoba, saboda ranar hutu ne a Najeriya."

KU KARANTA: Hukumar NSCDC ta sallami hafsan da aka gani a bidiyo yana wawason kayan abinci a Abuja (Bidiyon)

Bayan rikice-rikice da zanga-zanga, Birtaniya ta bude ofishin jakadancinta dake Najeriya
Bayan rikice-rikice da zanga-zanga, Birtaniya ta bude ofishin jakadancinta dake Najeriya Credit: @UKinNigeria
Asali: Twitter

KU KARANTA: Muƙarraban gwamnati ne suka hamdame tallafin COVID-19 - Gwamna Yahaya Bello

A bangare guda, Kwamishinan ƴan sandan Legas, Hakeem Odumosu, a ranar Talata, ya ce sun kama mutum 520 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da ƙone-ƙone, fashi, kisan da kuma mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya lokacin zanga zangar Endsars.

Mr Odumosu ya shaidawa yan jarida a hedikwatar Ikeja, cewa an kama masu laifin ne a laifukan da aka aikata sakamakon karya doka lokacin zanga zangar EndSARS.

Zanga zangar wadda aka fara ta lumana ta zama rikici ranar Litinin, 12 ga Oktoba, lokacin da wasu ƴan bindiga dadi masu raayin aikata laifi a inda ake zanga zangar a Surulure suka fara tada hargitsi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel