Zanga-zanga: An kama mutum 520 a Legas - Ƴan Sanda

Zanga-zanga: An kama mutum 520 a Legas - Ƴan Sanda

- Ana zargin masu laifin da laifukan da suka shafi lalata kayan gwamnati da na al'umma

- 'Yan sanda uku ne suka rasa rayukansu inda wasu da dama suka jikkata

- Zanga zangar lumana ce ta zama hargitsin da ya yi sanadiyar kama mutane 520

Kwamishinan ƴan sandan Legas, Hakeem Odumosu, a ranar Talata, ya ce sun kama mutum 520 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da ƙone-ƙone, fashi, kisan da kuma mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya lokacin zanga zangar Endsars.

Mr Odumosu ya shaidawa yan jarida a hedikwatar Ikeja, cewa an kama masu laifin ne a laifukan da aka aikata sakamakon karya doka lokacin zanga zangar EndSARS a cewar rahoton Premium Times.

Zanga zangar wadda aka fara ta lumana ta zama rikici ranar Litinin, 12 ga Oktoba, lokacin da wasu ƴan bindiga dadi masu raayin aikata laifi a inda ake zanga zangar a Surulure suka fara tada hargitsi.

Zanga-zanga: An kama mutum 520 a Legas - Ƴan Sanda
Zanga-zanga: An kama mutum 520 a Legas - Ƴan Sanda. Hoto Premium Times Ng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutum 13 ne suka rasu a hadarin mota a babban titin Kano zuwa Kaduna

Sun kuma ci gaba da kai hari kan manyan ma'aikatun gwamnati da guraren gwamnati da ofisoshin jami'an tsaro ta zargin kwance wasu barayin mutane a magarkama.

"A garin haka suka raunata yan sanda uku, tare da bude masu laifi guda biyu daga inda suke tsare, " a cewar kwamishina.

Odumosu ya ce Sifeto Erinfolamin Ayodeji da wani namiji mai wucewa, Mr Ikechukwu Ilohamauzo, sun gamu da hadarin harbin harsashi kuma daga bisani suka mutu a asibiti.

"Ya fito a fili cewa zanga zangar lumanar ta #endsars ta samu cikas daga bata gari," inji shi.

Yace kuma an kone ofisoshin ƴan sanda 16, an kuma lalata wasu 13, an kona motocin ƴan sanda 58 da sauran kayan mutane da dama.

Mr Odumosu ya ce an kashe jami'ai 6 na yan sanda kuma mutane 4 suka rasu a rikicin.

A dalilin hakan, yan sanda sun kama mutum 520 na laifukan da aka aikata.

KU KARANTA: EndSARS: Legos ta sake rikicewa yayin da yan tawaye suka lalata motocin BRT, suka fasa shaguna

Wani mai suna Olamilekan Ibrahim dan shekara 19,yana cikin wanda suka fasa wani sabon banki kuma ya kwashi kudi da wasu abubuwan amfani.

Kasonsa naira 250,000 a cikin abun da aka sato.

"Kuma wasu maza biyu da ake zargi, Ebere Ruben dan shekara 29, da kuma Samuel Oyediran me shekara 16 an kama su da zargin ƙona motocin BRT da gidan talabijin na TVC a Lagos," a cewar kwamishina.

A wani labarin, An ruwaito cewa mutum biyar sun rasu yayin da suka ƙoƙarin rabon wani adadin kudi da suka tsinta a maj'ajiyar abinci na gwamnati a Jalingo, jihar Taraba.

Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen sun ɓalle wurin ajiyar abincin ne inda suka tsinta jakuna biyu ɗauke da kuɗi ƴab dubu-dubu kusa da sakatariyar Kungiyar Kirista ta Najeriya a Jalingo ranar Asabar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel